Yadda zan gudanar da shugabancin Majalisar Dattijai idan an zaɓe ni- Sanata Lawan

45

Ɗan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar don yin takarar Shugabancin Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya yi alƙawarin yin aiki tare da abokan hamayya idan an zaɓe shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai.

Matsayin Sanata Lawan na baya-bayan nan ya saɓa da furucin da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Adams Oshimohole ya yi kwanan nan inda ya ce ba za a ba ‘yan hamayya shugabancin kwamitoci ba saboda jamiyyarsa ce za ta ɗauki mafi yawa daga cikin kwamitoci masu tsoka na Majalisar Dattijan ta 9.

To, amma mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Sanata Ahmad Lawan, Sanata Sabi Abdullahi ya roƙi sabbin sanatocin da aka zaɓa a karkashin tutar jam’iyyar PDP a wani taron manema labarai a Abuja da su yi watsi da waccan barazana.

Sanata Abdullahi ya ce Sanata Lawan, wanda ya kasance ɗan hamayya tsawon shekaru ya san irin damuwar abokan hamayya, kuma ba zai yi wani abu da zai cutar da su ba.

Ya kuma yi alƙawarin cewa Sanata Lawan zai yi aiki da dukkan sanatoci 109 da ake da su a matsayin wakilan al’ummarsu da girmamawa.

“Sanata Ahmad Lawan yana yin dukkan mai yiwuwa wajen tattaunawa da abokan aikinsa a dukkan jam’iyyu. Bari in faɗa muku cewa yadda Majalisa take waje ne da ba za ka iya yi wa kowa ihu ba. Ba zai yiwu ba.

“Ina so ‘yan Najeriya su kalli su waye ‘yan takara, su kuma yi amfani da abinda muke faɗa. Wannan shi ne abu mafi muhimmanci.

“Ina so in tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa idan Allah Ya yarda, idan Sanata Ahmad Lawan ya je wancan waje, zai gudanar da gwamnati ta kowa da kowa saboda Majalisar Dattijai Majalisar Dattijai ce ta Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.

“Sanatoci 109 da ake da su sanatoci ne ɗaiɗaiku dake wakiltar mazaɓun sanatoci daban-daban na Jamhoriyar Tarayyar Najeriya. Suna da dukkan wata dama da za a ji su kuma a saurare su don gwamnati ta yi musu aiki ba tare da kula da bambance-bambancenmu da son ranmu ba.

“Lokacin da muka ɗauki Rantsuwar Kama Aiki, mun yi alƙawarin cewa ba za mu bar buƙatar kanmu ta danne ta al’umma ba. Bari in bayyana a fili cewa burinmu shi ne a samu Majalisar Dattijai da za ta yi wa Najeriya aiki”, in ji Sanata Abdullahi.

Sanata Abdullahi ya ci gaba da cewa: “Na san idan aka duba tarihin Sanata Lawan tsawon shekaru 16 a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya fahimci matsalolin ‘yan adawa saboda ya kasance ɗaya daga cikinsu kafin yanzu, kuma ba zai ci mutuncin waccan alfarma ba.

“Saboda haka daga yanzu ya kamata a yi watsi da tunanin ɓangaren jam’iyyar PDP cewa za a mayar da su saniyar ware. Abinda muke tsarawa za mu yi shi ne a samu Majalisar Dattijai da za ta kasance ta dukkan sanatoci.

Sanata Abdullahi ya ce da yawa daga cikin sanatocin dake tunanin cewa Sanata Lawan ba zai yi tafiya da su ba a gwamnatinsa sun fara bayyana goyon bayansu tare da yin alƙawarin zaɓen sa ranar da za a ƙaddamar da sabuwar Majalisar Dattijai.

“Zan iya tabbatar muku cewa ranar da za a ƙaddamar da sabuwar Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan zai samu sama da biyu bisa uku na ƙuri’u daga dukkan sabbin sanatocin da aka zaɓa na APC da PDP da ba su gaza 73 ba.

“Muna ta magana da abokan aikinmu, k awo yanzu dai sai godiya. Mun gamsu sosai duba da irin karɓuwa da kamfen ɗimnu ke samu. Mun tuntuɓi da yawa daga cikin abokan aikimu sai dai waɗanda ba sa ƙasar nan”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan