Ba zama: Buhari ya shirya tsaf don ƙara tafiya wata ƙasar taro

182

A ranar Asabar ne Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa N’Djamena, babban birnin Cadi don halartar wani Taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Ƙasashen Yankin Sahel da aka yi wa laƙabi da CEN-SAD Meeting.

Garba Shehu, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman Kan Kafafen Yaɗa Labarai ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Mista Shehu ya ce Shugaban Buhari da sauran shugabannin yankin za su haɗu da mai ɗaukar nauyin taron kuma Shugaban Taron CEN-SAD na yanzu, Idriss Debby Itno don tattauna harkokin siyasa, tattalin arziƙi da sauransu.

Mista Shehu ya ci gaba da cewa shugabannin yankin za su kuma tattauna game da halin da zaman lafiya ke ciki, da kuma hanyoyin da za a warware tarin barazanar dake yankin CEN-SAD, musamman matsalar Boko Haram da ta ‘yan gudun hijira.
“A yayin buɗe Taron, za a ba da kyaututtuka na musamman ga shugabannin ƙasashe da rundunonin sojiji a Mali, Sudan, Somalia, Jamhoriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Ƙasashen Tafkin Cadi”, in ji Mista Shehu.

Ƙungiyar da aka kafa ta ta hanyar Yarjejeniyar Tripoli ranar 4 ga watan Fabrairu, 1988, Najeriya ta shiga Ƙungiyar Tattalin Arziƙin mai mambobi 29 a shekara ta 2001.

Yana daga cikin manufar Ƙungiyar ƙarfafa zaman lafiya, tsaro, daidaituwar al’amura da inganta tattalin arziƙi tsakanin mambobin ƙasashen.

Ana sa ran mambobin ƙasashe 22 ne za su halarci taron na CEN-SAD da za a yi a Radisson Blue Hotel dake N’Djamena.

Sudan wadda mamba ce ta ƙasashen na CEN-SAD ba za ta samu wakilci ba a taron sakamakon rashin tabbas na halin siyasa da aka shiga a ƙasar biyo bayan hamɓarar da Shugaba Omar al-Bashir da sojoji suka yi ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bada rahoton cewa da farko Shugaba al-Bashir ya nuna sha’awar halartar taron na CEN-SAD da za a fara daga ranar Juma’a zuwa Asabar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan