Yadda za a magance matsalolin tattalin arziƙin Najeriya- Sarki Sanusi II

228

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya yi kira da a samu manufofi da za su yi maganin matsalolin tattalin arziƙi da ake fama da su, su kuma sama wa ƙasar nan kyakkyawar makoma.

Basaraken gargajiyar ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi yayin wani taron tattaunawa da Ƙungiyar Masu Kamfanoni ta Ƙasa, MAN ta shirya a jihar Kano ranar Alhamis.

Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta mayar da hankali kan shirye-shirye da manufofi da za su tabbatar da bunƙasar tattalin arziƙi da ci gaba a ƙasar nan.

Ya ce haka kuma, akwai buƙatar gwamnati ta ɗau ƙwararan matakai da za su tabbatar wa ƙasar nan alƙibla mai kyau.

“Wajibi ne ga ‘yan siyasarmu su ba ƙasar nan abinda take buƙata. Ya kamata tunaninsu ya wuce na zaɓe mai zuwa.

“Yawan al’umma yana ɗaya daga cikin abubuwan dake ƙara talauci, saboda haka, akwai buƙatar mu dubi yadda muke fuskantar al’amura a ƙasar nan da gaske.

“Zaɓi ya rage namu, saboda matakin da za mu ɗauka yau shi ne zai saita alƙiblar ƙasar nan a gaba”, a cewar Sarkin.

Basaraken gargajiyar, wanda ya nuna damuwa bisa yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi musamman a Arewa da su mayar da ilimin firamare da sakandare ya zama kyauta kuma wajibi.

Ya ce ɗaukar wannan mataki ya zama wajibi don a rage ƙalubalen tattalin arziƙi dake addabar yankin musamman da kuma ƙasar nan gaba ɗaya.

“Muna da mutane dake rayuwa cikin talauci da yawansu ya fi talakawan dake rayuwa cikin talauci a India da China.

“Idan muna iya rayuwa da wannan yanayi, al’ummar da za ta zo gaba ba za ta iya rayuwa ƙarƙashin wannan yanayin ba, saboda haka dole gwamnati ta yi tunani a kan wannan, kuma ta yi wani abu cikin gaggawa”, in Sarki Sanusi.

A jawabinsa tun da farko, Shugaban MAN na Ƙasa, Injiniya Mansir Ahmed ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su haɗa guiwa da masu ruwa da tsaki don fuskantar tarin matsalolin dake addabar kamfanoni a ƙasar nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bada rahoton cewa masu ruwa da tsaki da dama ne suka halarci taron, da suka haɗa da wakilan Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Ƙasa, Bay Enterprise Limited da Shugaban Tsangayar Nazarin Ilimin Injiniya na Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan