Zafi kan zafi: Ministar Kuɗin Najeriya ta bayyana yadda Gwamnatin Tarayya za ta cire tallafin man fetur

168

Ministar Kuɗi ta Najeriya, Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin Tarayya za ta duba yadda za ta cire tallafin man fetur a hankali don haɓɓaka kuɗaɗen shiga.

Misis Ahmed ta bayyana haka ne a Washington DC, babban birnin Amurka a gefen tarukan tattaunawa da Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF da Bankin Duniya ke gudanarwa a halin yanzu.

Misis Ahmed na mayar da martani ne ga shawarar da IMF ya ba Najeriya da sauran ƙasashen da har yanzu suke bada tallafin man fetur da su daina.

A cewar IMF, cire tallafin man fetur zai taimaka wajen inganta kuɗin shiga, ya kuma ƙara wa gwamnati kuɗaɗe wajen gina ƙarin asibitoci, hanyoyi, makarantu, ta kuma tallafa wa ilimi da lafiyar jama’a.

“Shawara ce mai kyau. Amma muna buƙatar mu aiwatar da ita ta hanyar da za ta yi nasara, kuma ta ɗore.

“Ba mu da ikon da za mu tashi dare ɗaya mu cire tallafin man fetur.

“Dole mu ilimantar da jama’a, dole mu nuna wa ‘yan Najeriya yaya maye gurbin wannan tallafi zai kasance.

“To, muna da aiki da yawa saboda dole cire tallafin man fetur ya zama a hankali, kuma a wayar da kan al’umma sosai”, in ji Ministar.

Misis Ahmed tun da aka fara tarukan tattaunawa na IMF da Bankin Duniyar, ta yi tarukan ganawa manya-manya kan sa haraji da tattalin arziƙin duniya.

Ta ce: “Mun tattauna kan buƙatar gina ƙarin abubuwa da za a iya gani saboda tasgaron da tattalin arziƙin duniya ya samu da kuma yadda abubuwa ke faruwa a duniya kamar iska mai ƙarfi a Afirka ta Kudu

“Muna kan tattaunawa a tsakaninmu game da yadda za mu gudanar da harkokin kuɗinmu, da kuma yadda ya zama wajibi mu rage wa kanmu basuka.

“Ga Najeriya, muna roƙon Bankin Duniya da ya duba wasu shirye-shirye da zai haɗa su duba tsarin aiwatarwa yayin da za su samar da kuɗi don kayayyakin more rayuwa.

“Mun fahimci cewa za su yi shi ne da kyakkyawan niyya, amma mun sanar da su cewa suna buƙatar su duba aiwatar da shi, don kada mu yi ƙasa sakamakon sabbin ƙa’idoji.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan