Buhari ya dawo

471

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga N’Djamena, babban birnin ƙasar Cadi bayan halartar Babban Taron Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatocin Ƙasashen Yankin Sahel da ake yi wa laƙabi da CEN-SAD.
Waɗanda suka yi ban-kwana da Shugaban Ƙasar a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Hassan Djamous dake N’Djamena sun haɗa da jami’an gwamnatin Cadi, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje na Najeriya, Jeoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya da Ministan Tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya.

Sauran sun haɗa da Majo Janar Mohammed Monguno mai ritaya, Darakta Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa, Ambassador Ahmed Rufa’i Abubakar, Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, Mohammed Babandede da Kwamishiniyar Tarayya mai Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Sadiya Umar Farouq da Jakadan Najeriya a Cadi, Nasiru Waje.

Yayin da yake N’Djamena ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ankarar da taron bisa yadda ƙananan makamai ke shigowa Najeriya, yana mai cewa waɗannan makamai suna shiga hannun tsageru, ‘yan bindiga da ‘yan tada ƙayar baya waɗanda ke zama barazana ga haƙƙoƙin ɗan-Adam da tsaron cikin gida

Daga nan ya yi kira da a samu faffaɗan haɗin kai tsakanin Ƙasashen Yankunan Sahel da na Sahara don yin maganin shigowar waɗannan ƙananan makamai zuwa Najeriya.

Turawa Abokai

6 Sako

  1. Good post. I checked out your blog pretty often, and you’re
    always coming up with some good staff. I shared this
    blog post on my Facebook, and my followers loved it!
    Keep up the good work.

  2. Hi! This is my first visit to your blog! We are a collection of volunteers and starting a
    new project in a community in the same niche.
    Your blog provided us valuable information to work on. You have done a outstanding job!

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan