Ko mene ne martanin Atiku game da iƙirarin da APC ta yi cewa shi ba ɗan Najeriya ba ne?

253

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairun 2019, Atiku Abubakar ya ce kasancewarsa ɗan Najeriya ba abu ba ne da za a tsaya ana tababa a kai.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen watsa labarai, Paul Ibe ya fitar ranar Asabar.

Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC ta shaida wa Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓe cewa Atiku ba ɗan Najeriya ba ne, ɗan Kamaru ne.

A sanarwar, Atiku ya ce ba zai mayar wa da APC martani ba, yana mai karawa da cewa lauyoyinsa za su yi abinda ya dace a kotu.

Ya ce: “Maganar da APC ke yi ba mai kama hankali ba ce, kuma hakan yana bayyana yadda “ruwa ya ƙare wa ɗan kada” ne daga ɓangarensu, don haka maganar ba ta da muhimmancin da zan mayar da martani. Babu shakka, lauyoyinmu za su yi abinda ya dace a kotu.

“Amma, abinda nake son in jawo hankalin ‘yan Najeriya gare shi shi ne cewa ta hanyar wannan gurguwar dabara, jam’iyyar APC da ɗan takararta sun tabbatar da cewa ƙwace wa ‘yan Najeriya abinda suka zaɓa suka yi, kuma abinda za su kare kansu da shi kaɗai shi ne su yi yunƙurin kawo sabuwar ma’anar da ba ta cikin Tsarin Mulki na kalmar “ɗan Najeriya”.

“To, amma ina da ƙarfin guiwa game da tsarin shari’ar Najeriya da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Na aminta cewa Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen za ta dubi wancan zargi yadda ya dace. Dole mu ci gaba da riƙe imanimu da doka da kuma asalinnu, (Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekara ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima)”.

“Atiku Abubakar hidimta wa ƙasarmu ba ha’inci a ɓangarori da dama, tun daga aikin gwamnati, inda ya samu ci gaba ta hanyar cancanta zuwa ƙololuwar fagen da ya zaɓa wa kansa zuwa aikin gwamnati, inda cikin yaddar Allah ya zama Mataimakin Shugaban Tarayyar Jamhoriyar Najeriya.

“Haka kuma, ya bada ƙarfinsa da baiwarsa wajen bunƙasa ƙasarmu ta hanyar samar da dubban ayyuka na kai tsaye da waɗanda ba na kai tsaye ba”, in ji Mista Ibe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan