Ko Me Yasa Facebook, Da Instagram, Da WhatsApp Suka Daina Aiki?

39

Shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram, da manhajar sakkoni ta WhatsApp su fuskanci matsaloli na tsawon fiye da awanni uki a jiya lahadi, 14 ga watan Afrilu.

BBC Hausa sun rawaito cewa wani shafin intanet mai kuka da shafukan intanet na aiki ko fuskantar matsala Down Detector ya ce mutane a sassan duniyar nan dabam-dabam sun koka da rashin samun shafukan uku, wadanda dukkaninsu mallakin Kamfanin Facebook ne.

BBC Hausa sun kara da cewa lamarin ya fara ne daga misalin karfe 11 da rabi a agogon kasar Ingila inda masu amfani da Facebook suka rika samun sako da ke cewa wani abu ba ya aiki yadda ya kamata a duk lokacin da suka nemi bude shafin. Da misalin karfe biyu na rana, shafin ya sanar da cewa an warware dukkan matsalolin da suka addabi ayyukansa.

Wani kakakin Kamfanin ya fitar da wata gajeriyar sanarwa kamar haka, ‘A yi mana afuwa saboda dukkan matsalolin da ku ka fuskanta’. Kamfanin dai na Facebook bai ce uffan ba dangane da dalilin daina aikin da shafukan suka yi, kuna bai ambaci yawan mutanen da matsalar ta shafa ba.

A watan maris na bana, Facebook ya gamu da matsalar da ta sanya masu ziyartar shafukan Facbook, da Instagram, har ma da WhatsApp suka kasa shiga na tsawon fiye da sa a 24.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan