Ko yaushe Najeriya za ta cire tallafin man fetur?

221

Gwamnatin Tarayya ta ƙara nanata matsayinta game da cire tallafin man fetur, tana mai cewa ba ta da shirin cire tallafin a nan gaba kaɗan.

Ministar Kuɗi ta Najeriya, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka lokacin da take yi wa wakilan Najeriya jawabi kan sakamakon tattaunawarsu da masu zuba jari da cibiyoyi a Taron Tattaunawa da Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF da Bankin Duniya suka shirya a babban birnin Amurka, Washington DC.

Misis Ahmed tana mayar da martani ne ga shawarar da IMF ya ba Najeriya cewa ta cire tallafin man fetur.

“Ba wani shiri a zahiri na cire tallafi. IMF ya ce zai fi kyau mu cire tallafin man fetur, don mu yi amfani da kuɗin a wasu muhimman ɓangarori.

“A bisa ƙa’ida, shawara ce mai kyau, amma a Najeriya ba mu da wasu shirye-shirye a halin yanzu na cire tallafin man fetur, saboda har yanzu ba mu yi tanadin tsare-tsaren da za su ba mu dama mu cire tallafin mu kuma sama wa al’ummarmu sauƙi ba.

“Saboda haka, babu shirin cire tallafin man fetur.

“Za mu yi aiki da ƙungiyoyi da dama don nemo wani zaɓi idan har ya zama dole mu cire shi. Har yanzu ba mu zo matakin cire tallafin man fetur ba”, in ji Misis Ahmed

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan