Rasuwar Justice Mamman Nasir Babbar Rashi Ne Ga Kasarnan Inji Shugaba Buhari

113

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa na rasuwar marigayi Justice Mamman Nasir. Shugaban ya bayyana rasuwar tsohon Jojin Kotun Daukaka karan a matsayi babban rashin ga Kasarnan. Ya mika ta’aziyyarsa ta hannun mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa akan harkokin yada labari malam Garba Shehu.

Shugaba Buhari ya bayyana marigayi alkali Mamman Nasir a matsayin mutum wanda a zamaninsu suka yi amfani da ma’aikatun gwamnati domin bauta wa al’umma da kasa baki daya.

Ya kara da cewa alkalai irin su marigayin sun fi maida hankali wajen kare mutuncinsu da taimakon al’umma fiye da tara dukiya a lokacin da suke rike da mukamai a ma’aikatun gwamnati.

Bugu da kari, shugaban ya ce, idan muka yi duba ga tsarin rayuwarsa da kuma abin da ya mallaka, zamu tabbatar da gaskiyarsa da kuma kishin kasa. Wasu yan kasarnan suna suna daukar ma’aikatun gwamnati a matsayin dama ta hamdamar kudi amma mutane irinsu marigayi Justice Mamman Nasir sun fi maida hankali akan yi aiki da gaskiya fiye da tara dukiya a dare daya.

Shugaban kara da Cewa yin hakan ne ya ba su damar kare mutuncin kansu domin babu handama a zuciyoyinsu. Wadatar zuci ita ce sirrin rayuwar jin dadi ga ma’aikacin gwamnati domin kuwa rashin sa, shi ya ke sa mutane da dama hadama da babakere.
Daga nan ya yi kira ga Iyalan marigayin da su kasance masu alfahari da shi, saboda ya kafa tarihi akan gaskiya, wanda hakan abin alfahari ne ga kowanni dan Adam.

Shugaba Buhari ya tura wakilan gwaamnatin tarayya domin su je su yi gaisuwa ga Iyalan marigayin, da gwamnatin jihar Katsina da mutanen jihar baki daya bisa rashin daya daga cikin mutane da ake kwatance da su a masarautar Katsina.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan