Takarar Shugaban Majalisar Dattijai: Sanatocin PDP sun bayyana wanda za su zaɓa

243

Sabbin sanatoci da aka zaɓa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP sun yi watsi da takarar Sanata Ahmad Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai.

Sanata Lawan dai na samun goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da Shugabancin Jam’iyyar APC na Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Adams Oshimohole.

Sabbin zaɓaɓbin sanatocin waɗanda suka buƙaci a sakaye sunayensu sun tattauna ne da wasu zaɓaɓɓun ‘yan jarida don guje wa bi-ta-da-ƙulli daga gwamnati.

Sun lashi takobin zaɓen ɗan takarar da jam’iyyar PDP ke so a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai.

Sanatocin sun kuma lashi takobin yin watsi da yin amfani da Tsarin Zaɓe Buɗaɗɗe maimakon Tsarin Zaɓe na Sirri idan an zo zaɓen Shugaban Majalisar Dattijan.

Dokar Majalisar Dattijai da aka yi wa kwaskwarima dai ta amince da yin amfani da Tsarin Zaɓe na Sirri idan an zo zaɓen Shugaban Majalisar Dattijai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai.

Ɗaya daga cikin sabbin zaɓaɓɓen sanatocin ya ce jam’iyyar PDP za ta yi ruwan ƙuri’u ga duk ɗan takarar da zai tabbatar da cin gashin kan Majalisar Dattijai.

“Za mu yi ruwan ƙuri’u ga dukkan ɗan takarar APC wanda ba zai zama ‘ɗan aiken Ɓangaren Zartarwa’ ba”, in ji sanatocin.

Sabbin sanatocin APC biyu- Ali Ndume da Danjuma Goje sun nuna sha’awarsu ta yin takarar Shugaban Majalisar Dattijan.

Amma, da alama Sanata Ndume ya fi sauran ‘yan takarar ƙarfi.

A ranar Lahadi ne sabbin zaɓaɓɓen sanatocin na PDP suka ce za su fi so su zaɓi Sanata Goje ko Ndume, tsohon Jagoran Majalisar Dattijai, wanda sun yi amannar zai iya tafiya da mabanbantan ra’ayoyi, ya kuma tabbatar da cin gashin kan Majalisar.

“Hankalimnu ya fi kwanciya da ko dai Sanata Goje ko Ndume, amma ba Sanata Lawan ba, wanda ake gani a matsayin ‘ɗan aiken Ɓangaren Zartarwa’, a cewar sanatocin.

Dama dai tuni Sanata Eyinnaya Abaribe, wanda shi ma sabon zaɓaɓɓen sanata ne, da sabon zaɓaɓɓen sanata, Gabriel Suswan sun fito fili sun yi fatali da tsayar da Sanata Ahmad Lawan da Shugabancin Jam’iyyar APC ya yi.

Sanata Abaribe ya ce Majalisar ba za ta zauna ta ƙyale wani ya ƙaƙaba mata ‘Turawan Zaɓe ba’, yana mai nanata cewa zaɓaɓɓun sanatoci da aka tantance ne kaɗai za su yi zaɓe idan lokacin ya yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan