‘Yan bindiga a jihar Zamfara suna ganin ta kansu

51

Rahotanni sun ce an kashe mahara da dama ranar Lahadi lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka ƙaddamar da hari a ƙauyen Tsanu a dake yankin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Mazauna ƙauyen suka ce sojojin sun zo garin ne da misalin ƙarfe 1 na rana, ɗauke da muggan makamai, suka mamaye ƙofar shiga da ta fita garin, kafin su fara kai hare-haren.

“Yayin da aka jibge wasu sojoji a ƙofar shiga da ta fita ƙauyen, wasu sun shiga kasuwar garin ne, suna neman mahara dake yawo da makamai. Suka kashe da yawa daga cikinsu, yayin da wasu suka yi watsi da bindigoginsu suka tsere.

“Ba zan iya cewa ga yawan ‘yan bindiga da aka kashe ba, amma an kashe da yawa daga cikinsu, saura kuma sun gudu da raunukan harsashi a jikinsu. Lokacin da sojoji suka zo, sun iya gane ‘yan bindigar cikin sauƙi saboda suna ɗaga makamai”, a cewar wani mazaunin garin wanda bai buƙaci a bayyana sunansa ba.

A cewarsa, “Mun ga mahara guda huɗu da aka kama, ɗaya daga cikinsu yana da kemis a garin, wanda ana zargin shi ke ba maharan magani”.

Mai magana da yawun Rundunar Sojin a Zamfara, Clement Abiade, mai muƙamin Majo ya tabbatar da wannan rahoto. Ya ce amma ana ci gaba da kai da hare-hare a halin yanzu, saboda haka bayanai ba za su zama cikakku ba. Ya ce ba a yi adalci ba idan aka yi wani tsokaci a halin yanzu.

A ranar Asabar jaridar Premium Times ta kawo rahoton yadda mahara suka shiga ƙauyukan Jaja, Rukudawa da Tsanu a yankin ƙaramar hukumar Zurmi, suna tafiya ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba.

Rahotanni sun ce maharan suna tserewa ne bayan sojoji sun fara kai hare-hare ta sama a da yawa daga cikin maɓoyarsu a daji. Wasu mazauna ƙauyukan kuma sun karɓe su a cikin tsoro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan