Kasar Ingila ta gargadi mata da yan mata a kasarnan da su guji zuwa kasar ta barauniyar hanya domin yin hakan zai kaisu ga salwantar rayuwarsu ko kuma fadawa cikin bauta.
Gwamnatin kasar Ingila ta bayyana haka ta hannun wani kamfen mai taken ‘Mu Ba Na Sayarwa Ba Ne’ wanda kungiyar National Crime Agency da UK’s Joint Border Task Force, da Nigerian Law Enforcement suke tallafawa.
Shafin yanar gizo ta Independent.co.uk ta rawaito cewa suna amfani da labarai na cigaba na mata wanda suka zama wasu a kasarnan domin nuna ma mata illar irin wannan tafiyar.
Shafin ya kara da cewa ana amfani da labarin wata mata mai suna Gift Jonathan wanda ta yi kokarin zuwa kasashen turai ta barauniyar hanya bayan ta bar ýaýanta guda biyo a hannun mamanta a nan gida Najeriya, da niyyar neman kudi amma sai ta fada hannun masu safarar mutane a kasar Libiya a lokacin da ta ke kokarib zuwa kasar Jamus.
Gift ta ce tana ji tana gani aka siyar da ita a matsayin baiwa. Ta sha bakar azaba da wulakanci domin kuwa har fyade aka yi mata. Akan idanuwanta da yawa daga cikin abokan tafiyanta yan Najeriya suka rasa rayukansu, ita kanta da kyar ta samu ta kubuto zuwa gida Najeriya.
Ta kara da cewa a yanzu ta hakura da yawon neman kudi a turai, ta kama sana’ar gashin Biredi a jihar Benin kuma tana samun rufin asiri da ta ke kula da kanta da iyalinta. Ta ce a yanzu ta san ýaýanta zasu girma suna alfahari da ita.
Bincike ya nuna cewa kasarnan tafi kowacce kasa yawan mutane da suke faďawa cikin bauta a lardin Afrika a kokarinsu na tafiya kasashen taurai neman kudi.
Hukumomin UK Aid, da National Crime Agency, da Nigerian Law Enforcement suna iya bakin kokarinsu dan ganin an kawo karshen matsalar.