KUSKUREN BBC, MALAMAN JAMI’A DA MASANA HARSHEN HAUSA

383

Ali Abubakar Sadiq
aleesadeeq1@yahoo.com
08039702951

Tsawon tarihi an sami tsangayu a al’ummomi daban-daban, kama tun daga lokacin da babu rubutattun bayanai har lokacin da aka fara samun damar iya ajiye rubutattun bayanai domin ‘yan baya su amfana. Tsangayu, irin wadanda masana falsafa, Annabawa, shaihunnai da ɗarikoki na addinai suka samar, sun zama wata mattatara ta bada ilimi da yada shi da kuma adana shi. A yanzu muna da rubutattun bayanai na mashahuran masana falsafa da suka rayu dubban shekaru da su ka wuce irin su Aristotle, Ibn Rushd, Socrates da Annabawa irin su Musa, Isa da Annabi Muhammadu. Ɗan Adam kaɗai cikin halittun duniya ya sami wannan baiwa ta yin amfani da harshe ta hanyar rubutu domin samar da sashe na ilimi wanda a ke iya yaɗawa daga wannan zamani zuwa wancan.

Ginshiƙan ilimi su ne harshe da rubutu, shi ya sa mu ka ga umarnin farko da Allah ya bai wa Annabi Muhammadu shi ne na “Yi karatu”. Ilimi shi ne gudumar duka da tsinka sarƙar jahilci, ta yadda Ɗan Adam zai kai matsayin da Allah ya ba shi damar kaiwa. A zamanance, Jami’o’i su ne tsangayu da su ka gaji turakan sadar da ilimi da aka gada domin ilimintar da al’umma. Jami’ar Al’Azhar da ke Misra ta zama cikin sahun farko na tsangayar ilimi ta zamani wadda daga baya a ka fara samun jami’o’i a Turai. Jami’ar Oxford dake ƙasar Ingila ta kasance jami’a ta uku a Turai wadda a ka kafa a farkon karni na 12. Wannan jami’a ta duƙufa wajen ganin ta samar da cikakken Ƙamus na Turanci kasancewar Turanci, sakamakon faɗaɗar Daular Birtaniya ta mamaye kusan kaso ¼ na faɗin duniya, yadda yaren Ingilishi ya zama yare mafi girma da a ke amfani da shi a duniya (Global Lingua Franca).

Wannan yunƙuri na jami’ar Oxford da ƙoƙarin samar da cikakken Ƙamus na yaren Turanci zai nuna maka cewa ita jami’a, aikinta na farko shi ne bincike da yada ilimin al’ummar da take wakilta. A duk inda jami’a ta ke aikinta shi ne yin nazarin matsalolin wannan al’umma da samo mata hanyoyin magance waɗannan matsaloli nata, kuma abu ne wanda ke wanzuwa yau da gobe. Don haka matsaloli na fannonin Harshe, Kasuwanci, Gine-gine, Zamantakewa, Addini, Siyasa, Lissafi, Kimiyya, Tattalin Arziƙi, Kiwon Lafiya, Yaɗa Labarai, kai da duk wani fanni da ya ke da tasiri a al’umma, alhakin jami’ar Bayero ta Kano ne ko Ahmadu Bello dake Zariya ne su yi bincike da samo hanyoyin kawo maslahohi ga al’ummar Kano da Zaria, da Najeriya da ma duniya gaba ɗaya. Wannan shi ne ruhin da ya kamata kowacce jami’a ta ɗauka, amma sanin kowa ne saɓanin haka jami’o’inmu ke kai a yanzu. Mu a nan Najeriya, amfanin jami’a shi ne kasancewa hanya tilo ta samar wa ɗalibai tikitin neman aikin yi bayan gama jami’a, su kuma malamansu ya zama hanya ta neman abinci domin samun kambama a wajen ɗalibai da al’umma. Wannan dalili ya sa babu komai cikin ɗakunan binciken jami’o’inmu kuma ba wani abin ƙirƙira da ke fitowa daga cikinsu, sai fankama ta malamai masu digirin-digirgir.

Yaren Hausa ya kasance yare na 11 mafi girma a duniya, da kimanin mutane miliyan 150 masu yin amfani da shi, wato ya zarta yaruka irin su Japanese, German da Swahili, amma abin kunya shi ne babu wata jami’a dake ƙasar Hausa wadda a yau take da wani ƙamus na Hausa kamar yadda na kawo misalin Ƙamus ɗin Jami’ar Oxford wanda shi ne ja-gaba a duniya. Sannan babu wani mashahurin masanin Hausa wanda ya yi irin wanna aiki. Duk ƙamus ɗin da ake da su a Hausa a yau, za ku ga cewa Turawa ne su kai mana wannan aiki. Haka zalika, a duk sauran sassa na ilimi idan ka ga wani mashahurin littafi to za ka ga cewa Bature ne ya rubuta shi. Hatta rubuce-rubucen tarihin magabata za ka samu cewar Turawa su ka rubuta mana yawancinsu.

A rubu’in farko na wannan shekara ta 2019, Ƙamus din Turanci na Jami’ar Oxford ya shigar da sabbin kalmomi sama da 600 kuma cikin wannan ƙamus akwai kalma guda wadda wajen fassara ta an yi amfani da kalmomi 60,000 (wato kusan littafi guda) domin ana amfani da ita ta hanyoyi sama da 400. Shi yare a kullum haɓaka yake sakamakon hanyoyi guda 5 da yake ta’ammali da su. Na farko shi ne hanyoyin mu’amala da wasu yaruka (Foreign) wanda hakan na cusa sabbin kalmomi cikin yare, sannan yadda ake samun banbancin harshe (Dialect) daga mutanen dake yin yare guda shi ma kan kawo sabbin kalmomi (misali Kananci da Sakkwatanci) da kuma irin kebantuwa na masu yare (Slang) saboda tattalin arziki, shekaru ko sana’a na haifar da sabbin kalmomi. Haka kuma akwai ci gaba na Ƙere-ƙere da Fasaha (Technological) wadanda a kullum ke samar da sabbin kalmomi, sannan a karshe akwai fannin Kimiyya (Scientific) shi ma wanda ke da irin wannan tasiri domin kullum faɗaɗa bincike da nazari a ke yi wajen gano sabbin abubuwa.

Wannan gaba ita ta kawo ni ga Babban dalilin yin wannan rubutu, domin a cikin ‘yan kwanankin nan Ɗan Adam ya cimma wani mizani a Ilimin Sararin Samaniya (Astronomy) wanda bai taɓa cimma ba a baya. Wannan ci gaba shi ne na samun damar iya ɗauko hoton Baƙar Tauraruwa, abar da masana Kimiyya suka yi shekaru ɗaruruwa suna hasashen samuwar ta, wanda sai yanzu a ka gan ta ido da da ido. Gidan Rediyon BBC ya yi hira da wani masani a wannan fanni, wato Aliyu Dahiru wanda suka tambaye shi da me ya kamata a fassara “Black Hole” a Hausa? Inda ya ba su amsar cewa za a iya fassara ta da “Mutuwaren Taurari”. Ina ganin akwai gyara wajen yin wannan fassara da kuma yaɗa amfani da wannan fassara domin ta yi karo da wasu hujjoji da nake son mu kalla. Na farko dai mun yarda, kamar yadda na kawo a baya cewar cikin hanyoyin ɗaukar sabbin kalmomi a harshe akwai maganar aro daga wani harshe. Malam Aliyu Dahiru ya yi amfani da wannan hanya wajen aro Kalmar “Mortuary” daga Turanci wajen fassara Black Hole da Mutuwaren Taurari. To amma ba ka aron baƙuwar kalma idan kana da ita a cikin harshenka. Misali a Turanci, mun san cewa al’adar Bature, kamar yadda Bahaushe ke cewa “Idan ka ga zara ka ga wata”, Bature nada kalmomi ‘yan tagwaye na “Table” da “Chair” amma a Hausa mu kuma al’adarmu ba mu da Table, don haka da Bature ya kawo kalmomin guda biyu lokacin mulkin mallaka, sai mu ka ari kalmar “Table” muka fassara ta da “Teburi” domin ba mu da ita, amma kuma ba mu ari “Chair” ba saboda muna da ita, wato “Kujera”.

Idan mu ka koma kan fassarar Black Hole, a Kimiyyance shi Black Hole asalinsa duk inda ka gan shi tauraruwa ce wadda saboda nauyi da ƙarfin maganaɗisunta, ya sa ta dunƙule yadda ko haske ba ya iya fita daga cikinta. Taurari, kamar halittu masu rai suke domin suna da tsarin haihuwa, yarinta, tsufa da kuma mutuwa. A cikin tsarin aji-aji na wanzuwar tauraruwa, idan ta kai wani mizani wanda ba za ta iya ci gaba da rayuwa tare da watso haskenta saboda nauyinta ba, sai ta dunƙule waje guda ta takure yadda karfin maganaɗisunta ba zai iya barin ko da haske ya fita daga cikinta ba. Ko da wannan tauraruwa ta haɗiyi wani tauraron ko ba ta haɗiya ba tana nan a matsayin tauraruwa wadda ido ba zai iya ganin ta ba. An yi shekaru ana hasashen samuwar ta sai a wannan karo masana suka sami damar ɗauko hotonta. Dalilin da yasa a ka yi hasashen samuwar ta kuwa shi ne saboda yadda a duk inda take a ke ganin halittu na ɓacewa, saboda duk abinda ya zo kusa da ita, tana laƙume shi. Wannan halayya ta sa aka fara laluben inda irin waɗannan taurari suke. Kuma sakamakon idan ta wafce wasu halittu, irin su hayaƙi (gas) ko tauraro (star) ko kuma dunƙulen halitta (matter) daga cikin abinda ba ta wafta ya faɗa cikin ta ba, yakan ƙone wanda sakamakon wannan ƙonewar ke haifar da haske mai ƙarfin gaske a kewayen tauraruwar (Accretion disk). Wannan yanayi shi ne Babban Madubin Hangen Sararin Samaniya na EHT (Event Horizon Telescope) ya sami damar ɗauko hoton, yadda duniya a karon farko ta ga yadda Bakar Tauraruwa take. Akwai wasu taurarin kuma dake da nauyi da idan suka kai irin wannan matsayi, maimakon su ɗunƙule su ɓace, sai su yi bindiga su tarwatse yadda za su watsar da mafi yawan haskensu (Supernova) su koma su takure (Neutron star) su ci gaba da rayuwa tare da bayar da haske ƙalilan yadda da ƙyar a ke iya hangen su. Misali mai sauƙi da mutane za su gane shi ne ta hanyar fitilar ƙwai, idan kana zuba mata kananzir ya yi yawa, wani lokaci sai fitilar ta yi but-but ta mutu (misalin Black Hole kenan), amma wani lokacin idan ta yi but sai haskenta ya ninninka kafin ta koma daidai ta ci gaba da ci (misalin Supernova da ke zama Neutron Star kenan). Mutuwar taurari ba siffa guda ya ke bi ba, ya danganta da irin nauyin tauraruwar da girmanta. A dalilin haka na ke ganin babu dalilin da za a ari kalmar mutuware wajen fassara irin waɗannan taurari baƙaƙe da ido ba ya iya gani domin mahimmin aikinsu ba kashe taurari ba ne, illa dai duk tauraron da ya doshe su, sunansa matacce domin za su laƙume shi. Sannan wasu taurarin ba ta wannan hanya su ke mutuwa ba, akwai ma waɗanda idan sun zo mutuwa sai su manne da wani tauraron yadda wadannan taurari biyu da su ka haɗe, za su samar da wata sabuwar tauraruwar. A ganina, bisa waɗannan hujjoji, cikkakiyar fassararsu za ta kasance “Bakar Tauraruwa” domin ba a iya ganin su saboda ba sa barin haske ya fita, don haka sun kasance baƙiƙkirin amma ba “Mutuwaren Taurari” ba.

Matsayin Gidan Rediyon BBC nada mahimmanci a yaren Hausa ta zamani, kasancewar suna bada gudunmuwa wajen samar da fassarar kalmomi da musamman suka jiɓanci Kimiyya da Fasaha da zamananci. Don haka wajibi ne sassan binciken harshen Hausa, musamman na Jami’o’in Bayero da ABU tare da masana dake ciki da wajen jami’o’inmu, da haɗin kan BBC su samar da wata dama da Hausawa manazarta za su haɗu su samar wa da ‘yan baya cikakken Ƙamus na Hausa wanda ya fito daga hannun masana Hausawa. Sannan ya kasance a kowane fanni na ilimi (Musamman a kimiyya da Fasaha waɗanda suke haɓaka a gurguje) a sami masana da za su riƙa tantance sabbin kalmomi da za a riƙa sakawa cikin Kundin Ƙamus na Hausa lokaci-lokaci. Abin kunya ne a ce harshe mai mutane miliyan 150 da masana na kowane fanni a doron duniya, ya kasance sai dai baƙi daga waje su yi masa aiki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan