Martani: Shari’ar Musulunci Kariya Ce Ga Al’umma Inji Gwamnatin Brunei

171

Gwamnatin Kasar Brunei ta ce kaddamar da shari’ar musulunci da ta yi a matsayin kundin tsarin mulkin kasar wata hanya ce ta kare al’umma a maimakon matakin daukan hukinci mai tsanani da wasu ke zargi.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ce ta bayyana haka a matsayin martani biyo bayan soke-soke, da Allah wadai da gwamnatin ta fuskanta daga kasashen duniya akan kaddamar da shari’a a matsayin tsarin mulkin kasa a makon da ya gabata.

Ministan harkokin wajen kasar Erwan Yusuf ya kara da cewa bin tafarkin shari’a hanya ce na ilmantarwa, da gyara halaye da kulawa ga al’umma ba wai yin hukunci mai tsauri ba. Bugu da kari, haramta zina da luwadi wani mataki ne na kariya ga iyali da musulmi ma’aurata musamman mata.

Kasar ta Brunei ta zartar da doka inda zata yi hukuncin kisa ta hanyar jifa ga duk wanda aka kamma da laifin zina, da luwadi, da kuma hikuncin haddin sata na yanke hannu.

Hakan ya sa majalisar Dinkin Duniya (UN) ta yi kakkausar suka ga matakin, wanda ta kira shi a matsayin zalunci da keta haddin dan Adam.

Amma kasar ta Brunei ta kare kanta inda ta ce bawai zata yanke hukuncin ne kawai ba, dole sai an samu kwararan shehu maza akalla guda uku wanda kowa ya sheda mutanen kirki ne kafin a zartar da hukuncin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan