Kwamishinan Yansandar Jihar Zamfara Mista Celestine Okoye ya ce jami’an tsaro ba zasu yi batun sasantawa da yan ta’addan da suka addabi mutane a jihar ba.
Mista Okoye ya bayyana matsayar na jami’an tsaro bayan kammala taro akan tsaron jihar Zamfara a Talatar-Mafara.
Ya kara da cewa babu batun tattaunawa ko sasantawaba tsakanin su da yan ta’addan saboda jami’an tsaro sun shirya tsaf domin fatattakarsu daga jihar.
Kwamishina Celestine ya ce aikin ta’addanci a jihar Zamfara ya zo karshe amma a yanzu ba zasu bayyana matakan da zasu bi ba wajen kawar da su.
Turawa Abokai