Rikicin Zamfara: Da Alamu Akwai Sa Hannun Sarakunan Gargajiya A Lamarin

162

Wani bawan Allah ya yi karin bayani kan yadda zargin gwamnatin tarayya yake da kanshi gaskiya bayan ya ce mutane na zargin sarkin Zurmi da hannun a cikin rikin jihar Zamfara.

Biyo bayan zargin gwamnatin tarayya akan wasu masu rike da sarautun gargajiya da hannu cikin rikicin jihar Zamfara, ta bakin ministan tsaron kasa Mansur Dan Ali, Jaridar Premium Times ta saki wani rahoto da ta tattauna da wani mazaunin jihar wanda ya ce akwai alaka tsakanin masu rike da masarautun gargajiya da yan ta’addan da suka addabi jihar.

Jaridar Premiun Times ta rawaito mutum wanda ba a bayyana sunan sa ba , ya ce a shekarar 2016, lokacin da sarkin Zurmi ya aurara da ýaýansa mata guda hudu, kusan dukkan shahararrun ýan bindigan da aka sani sun halarci taron bikin kuma su suka bayar da gudunmuwan dabbobin da aka yanka a bikin.

Bugu da kari, a lokacin bikin an gayyaci wani shahararren mawakin barayi mai suna Sani Danyaya daga kasar Nijar, wanda ya kwashe akalla kwanaki biyu yana yiwa yan bindigan waka tare da karuwansu a garin Zurmi.

Ya kara da cewa fito na fito tsakanin sojojin da yan ta’addan ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba, don haka ya bawa rundunar sojojin kasa shawara da su shiga cikin garin Zurmi don jin ta bakin jama’a kan yadda yan ta’addan ke gudanar da aiyukkansu domin mutane a shirye suke su bawa gwamnati hadin kai saboda Karamar Hukumar Zurmi na daga cikin wanda suke fama da wannan matsala.

A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta fito da wata sanarwa wanda ministan tsaro Mansur Dan Ali ya ce rahoton sirri da suka samu ya nuna cewa akwai hannun sarakunan gargajiyar jihar Zamfara a cikin kashe-kashe da ke faruw. Amma hakan bai yiwa sarakunan dadi ba kuma sun nuna bacin ransu inda suka kalubalanci ministan da ya fito ya bayyana sunayen sarakunan da ya ke nufi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan