Rikicin Zamfara: Gwamnatin Jihar Ta Yabawa Kokarin Gwamnatin Tarayya

107

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yabawa kokarin gwamnatin tarayya bisa kokarinta na kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa Gwamna Abdulaziz Yari ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya bayan ya fito daga taro akan tsaron jihar. Ya ce gwamnatinsa tana maraba da manufofin da gwamnatin tarayya ta fitar domin tallafawa al’ummar jihar Zamafara.

Ya kara da cewa masu hakar ma’adanai a jihar suna yi ne ba bisa ka’ida ba kuma ana aikin hakan ma’adanan a kusa da sansanin Ýan ta’addan ba tare da su taba fuskantar wani matsala ba. Don haka dole ne a zarge su da hannu a cikin aikin yan ta’addan.

Daga nan, gwamna Yari ya yi kira ga al’ummar jihar da su bada gayan baya ga tsare-tsaren gwamnatin tarayya da na jami’an tsaro domin tabbatar da samun nasarar manufofin.

A karshe, ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya na aika jami’an tsaro jihar domin kawo karshen aikin ta’addanci a kuma hakan ya fara nuna sakamako mai kyau.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan