An Garkame Tsohon Shugaban Kasar Sudan A Gidan Yari

144

A yau an kai tsohon shugaban kasar sudan, Omar Al-Bashir gidan yarin Kobir mai cike da tsaro, bayan da sojohin suka hambarar da shi a mulki a kwanaki kadan da suka wuce.

BBC Hausa sun rawaito cewa kafin wannan lokaci, an tsare shugaba Al-Bashir bisa daurin talala a fadar shugaban kasa. Hakan ya biyo bayan watanni da aka shafe ana zanga-zanga a kasar daga baya sojoji suka hambarar da shi a ranar alhamis.

Kafin wannan lokaci, ba a san inda ake tsare tsohon shugaban kasar amma jagoran juyin mulkin Awad Ibn Auf ya ce ana tsare da shi ne a wani amintaccen wuri.

Daga baya, shi ma sai ya sauka daga mukaminsa sai aka nada laftanal janar Abdel Fattah Abdel Rahman Burhan a matsayin shugaban gwamnati na rikon kwarya. Hakan ya sa ya zama shugaban Sudan na uku a cikin yan kwanaki.

Masu zanga-zanga dai sun sha alwashin cigaba da mamaye tituna har sai an samu sauyin mulki zuwa farar hula.

Ministan harkokin cikin gida na Uganda Henry Oryem Okello ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa kasarsa zata duba yiwuwar baiwa Al-Bashir mafukar siyasa.

Duk da sammacin da kotun hukunta masu aikata miyagun laifuka ta duniya (ICC) ta aike masa. Kasar Uganda tana daga cikin mambobin kotin ICC, don haka ya zama dole ta mika Al-Bashir ga kotun idan har ya shiga kasar.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. I used to be very happy to find this web-site.I needed to thanks in your time for this excellent learn!! I positively having fun with every little little bit of it and I’ve you bookmarked to check out new stuff you weblog post.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan