Atiku ya samu hujja mai ƙarfi dake nuna cewa shi ya ci zaɓe

208

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nanata cewa sakamakon zaɓen dake babban shafin Intanet na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ya nuna cewa shi ne ya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen shugaban ƙasar.

A ƙarar da ya shigar a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa, Atiku ya bada adireshin shafin Intanet na INEC inda sakamakon ya fito.

Sakamakon zaɓe na jihohi 36 da Birnin Tarayya, Abuja da INEC ta bayyana ya nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’a 15,191,847 yayin da Atiku ya zo na biyu da ƙuri’a 11,262,978.
Amma a ƙarar da ya shigar a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa, ɗan takarar jam’iyyar ta PDP ya yi iƙirarin cewa ya samu kuri’a 18,356,732, inda a cewarsa ya doke Buhari wanda ya samu kuri’a 16,741,430.
Da take mayar da martani, INEC ta ce sakamakon da Atiku ya kawo ba daga shafinta na Intanet yake ba, ƙirƙiro shi aka yi.

A martaninsu ga INEC, wanda jaridar The Cable ta samu kwafi, Atiku da jam’iyyar PDP sun ce INEC kaɗai ke da irin adireshin Intanet ɗin da aka samo sakamakon.

Atiku da jam’iyyar PDP sun bada adireshin Intanet ɗin da suka samo sakamakon zaɓen kamar haka 94-57-A5-DC-64-B9 with Microsoft Product ID 00252-7000000000-AA535.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan