Home / Cigaban Al'umma / Farin jinin El-Rufa’i na neman jefa shi a matsala

Farin jinin El-Rufa’i na neman jefa shi a matsala

An bayyana Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna da takwaransa na Jihar Kano, Dakata Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ‘yan siyasar da suka fi kowa yawan asusun Facebook na bogi, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Binciken, da Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa, CITAD ta gudanar ya nuna cewa Gwamna El-Rufa’i yana da asusun Facebook na bogi 161 a watan Nuwamba, daga nan suka koma 172 a watan Disamba, inda suka kai 225 a watan Janairun 2019, yayinda Gwamna Ganduje ke da asusun Facebook na bogi 154 a watan Nuwamba, yayinda suka kai 168 a watan Disamba.

CITAD ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya ranar Laraba a ofishinta dake Kano.

Daga nan, Jami’in Kula da Kalaman Ɓatanci da Tunzura Jama’a a Cibiyar, Malam Hamza Ibrahim ya yi kira ga duk waɗanda abin ya shafa musamman ‘yan siyasa da su nemi ƙwararrun masana domin ba su shawarwari, kan matakan da ya kamata su ɗauka, da kuma hanyar da za su bi don kare ƙara faruwar hakan.

Hamza Ibrahim – Citad Kano

A cewar Malam Ibrahim, mutanen dake amfani da sunan ‘yan siyasar na iya haddasa rikici ta hanyar wallafa rubutu a shafukan da sunansu, alhali ba su ba ne a zahiri, ko kuma su damfari abokansu a shafukan sada zumunta.

About Hassan Hamza

Check Also

Ƴan Bindiga sun yi awon gaba da wasu tarin jama’a a lokacin da su ke sallar Tuhajjud a Katsina

Wasu rahotanni daga jihar Katsina sun bayyana cewa kimanin mutane arba’in da su ka haɗa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *