Hukumar JAMB Ta Ce Dalibai Da Dama Ba Zasu Samu Sakamakonsu Ba Saboda Laifin Satar Amsa

166

Hukumar shirya jarabawa share fagen shiga jami’a (JAMB) ta ce dalibai da dama da suka zana jarrabawar a wannan shekara ba zasu samu sakamakon jarrabawar ba saboda kama su da laifi satar amsa.

Shugaban hukumar ta JAMB farfesa Ishaq Oloyode ya bayyana haka a jiya laraba a jihar legas a lokacin da ake kama wasu mutum biyu mutum biyu da laifin sayar da amsar jarrabawar na bogi ga jama’a

Mutanen biyun masu suna Godswill Ukpai da David Ukpai ýaýa ne ga wani mutum da ya ke da cibiyar zana jarrabawar UTME. Masu laifin biyu sun amsa laifin daukan hoton tambayoyi da amsoshin su daga cibiyar zana jarrabawar na mahaifinsu kuma sun sayar wa wani mutum mai cibiyar koyar da jarabawar mai suna Embasy a jihar legas.

A lokacin kamen, an hada da wani mutum mai suna Obinnq Ebere wanda ya ke kula da sashin fasaha cibiyar wanda ya amsa laifi irin na yaran biyu. Masu laifin sun bayyana cewa suna sayar da tambayoyin da amsoshinsu ga mutumin mai cibiyar Embassy, shi kuma sai ya kawo musu dalibai cibiyarsu domin yin rijista da zana jarabawar UTME.

Mahaifin yaran ya bayyana takaicinsa kuma ya ce tunda sun kai shekarun da zasu iya fuskantar hukunci, to a yi musu hukunci dai-dai da laifukansu.

Shugaban hukumar JAMB ya ce sun samu nasarar kama masu laifin ne bayan sun saka na’urar CCTV, mai daukan hoton sirri da ke hade da hedkwatan hukumar.

Bugu da Kari, bayan alifin karya doka da suka yi na shiga ajin jarrabawar a lokacin da yake gudana, har da laifin sayar da jarrabawar bogi domin hukumar bata maimaita jarrabawar kowani dalibi sai bayan shekaru biyar.

Farfesa Oloyode ya ce sun kama mutane dari da suke zargin satar amsar jarrabawar na bana. Wannan na daya daga cikin hanyoyin the hukumar ta ke bi don tabbatar da gaskiya da sahihancin jarrabawar.

Ya kara da cewa a bana, dubunnen dalibai ba za su samu sakamakon jarrabawarsu ba, saboda an kama su da laifukan da suka saba dokar jarrabawa a hotunan CCTV daga cibiyoyin zana jarabawar guda 700. Sannan ya sanar da hukuncin dakatar da wannan cibiya kuma an daga jarabawar daliban da ke cibiyar zuwa wasu cibiyoyin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan