Jami’an tsaro sun sako wani jigo a Kwankwasiyya da suka kama a Kano

171

Salisu Hotoro, wani ɗan Kwankwasiyya da jami’an tsaron Farin Kaya na SSS suka kama a gidansa dake Hotoro a jihar Kano ranar 4 ga watan Afrilu ya samu ‘yanci.

Hafizu Bichi, lauyan Mista Hotoro ne ya tabbatar wa da jaridar Daily Nigerian sakin nasa ranar Talata da yamma.

Mista Hotoro ne babban mai sukar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa an kama shi ne bisa zargin ɓata wa tsohon Manajan Daraktan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA, Aminu Dabo suna.

Tsohon Manajan Daraktan ya fusata ‘yan Kwankwasiyya da ya ce shi yake ‘ɗawainiya’ da ‘yan Kwankwasiyya kafin ya canza sheƙa zuwa APC.

Da yake tsokaci game da sakin Mista Hotoro, Sanusi Dawakin Tofa, mai magana da yawun ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da abinda ya kira ‘wannan tsoratarwa dake ake yi wa ‘yan adawa daga maƙiya dimokuraɗiyya’.

A cewarsa, kama Mista Hotoro wata kutungwila ce daga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da jam’iyyar APC na su takura masa.

Ya lashi takobin cewa wannan tsoratarwa ba za ta hana ‘yan hamayya ci gaba sukar Shugaba Muhammadu Buhari da Mista Ganduje bisa rashin adalcin da aka yi musu a zaɓen gwamna zagaye na biyu ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan