Yawan Amfani Da Wayar Zamani Da Yanar Gizo Yana Haifar Da Illa Ga Lafiyar Matasa – Ma’aikatan Lafiya

97

Kwararru akan harkar lafiya sunyi gargadi bisa yadda ake samun karuwar amfani da wayoyin zamani da shafukan yanar gizo a hannun matasan kasarnan.

Kwararrun sun bayyana hakan ne a lokacin da ake gudanar da tari na kasa akana lafiyar matasa da cigabansu a kasarnan. Taron ya yi jan hankali ga iyaye, da makarantu, da gwamnati, da su sanya idanu akan yadda matasa ke amfani da yanar gizo.

Taron wanda kungiyar matasa mai suna Society For Adolescent and Young People’s Health in Nigeria ( SAYPHIN) ta shirya har na tsawon kwana uku a dakin taro na cibiyar Subomi Balogun da ke Jami’ar Ibadan.

Wani likitan kwakwalwa mai suna Segun Mathew ya yi bayanin cewa yawan amfani da yanar gizo ga matasa na da hadari ga lafiyarsu. Don haka ya ce abu ne mai saauki matasa su zama sun saba da wayoyi fiye da kima, su shaku da su kuma hakan zai iya haifar da matsala ga kwakwalwarsu.

Ya kara da cewa yawan amfani da matasa suke yi da yanar gizo don sadarwa, da nishadi, da sauran bukace bukacen su yana sa su samu shakuwa da yanar gizo a kananan shekaru kuma hakan yana shafar yanayin halayyarsu, da dabi’un su a rayuwa.

Don haka ma’aikatan lafiya suka ce shakuwa da yanar gizo da yawan ta’ammali da shi zai iya haifar da yanayin damuwa watau depression, da sauran cututtuka da ya shafi kwakwalwa.

A yayin bude taron ministan ilimi na kasa mista Isaac Adewole wanda shugaban asibitin koyarwa na Obefemi Awolowo, Victor Adetiloye ya wakilta ya ce jigon taron na bana wani mataki ne na tabbatar da cigaban matasa a kasarnan.

Shugaban kungiyar SAYPHIN kuma farfesa a likitance, mista Fatusi ya ce yana fatan wannan mataki zai taimaka wajen kawo cigaba a lafiyar matasa a kasarnan. Matasa da dama a kasarnan suna fama da cututtuka kaamar su cutar Kanjamau, da shaye-shaye, da sauran miyagun dabi’u a kasarnan, kuma hakan ba abun alfahari ba ne. Don haka sun shirya taron dan gayyato masu ruwa da tsaki don samar da mafita da zai kawo cigaba a harkar lafiyar matasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan