A jiya Laraba ne da misalin ƙarfe 12 na dare, Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS ta buɗe shafinta na Intanet don ɗaukar sabbin ma’aikata da yawansu ya kai 3,200 waɗanda za su cike guraben aiki da ake da su a Hukumar.
A cewar Hukumar, ta bakin Muƙaddashin Kwanturola Janar ɗinta, Sani Umar, shirin ɗaukar sabbin ma’aikatan ya samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC, kuma yana kan ƙa’idojin Hukumar Kula da Ɗaukar Ma’aikata ta Ƙasa, FCC.
Mista Umar ya ce za a gudanar da ɗaukar ma’aikata aiki ne don a cike guraben mutum 800 da ake da shi a ɓangaren Support Staff for Superintendent Cadre, yayinda za a ɗauki mutum 2,400 a ɓangaren Customs Inspector and Customs Assistant Cadre a General Category.
Hukumar ta ce masu buƙatar aikin za su iya ziyartar www.vacancy.customs.gov.ng don neman aikin.
Hukumar ta ce shafin nata na Intanet zai kasance a buɗe tsawon makonni uku.
“Mun ƙudiri aniyar gudanar da wannan aiki cikin adalci da yin komai a fili. Za mu yi amfani da dukkan matakai da muke da iko a kai don tabbatar da cewa ba a zubar da mutuncin tsarin ɗaukar aikin ba”, in ji Mista Umar.