Ofishin Jakadancin Kasar Canada da ke kasarnan ya karyata labarin da ke cewa kasar ta Canada tana bukatar yan cira ni har miliyan daya.
Ofishin jakadancin ya musanta wannan labari na bogi a wani sako da ya saka a shafinsa na Twitter. Sakon yana cewa ‘Idan ka ci karo da wannan labari a shafin ka na sada zumunta, to ka sani ba gaskiya ba ne. Domin samun bayanai kan balaguro zuwa Canada, ka ziyarci wannan shafin’.
Ofishin ya kara da cewa a shekarar 2017 kadai, an baiwa yan Najeriya 4,200 shaidar zama a kasar ta din-din-din, wanda ya ninka yawan wadanda aka baiwa a shekarar 2016. Yan Najeriya mazauna kasar Canada suna bai wa kasashen biyu kyakkyawar gudunmuwa.
A farkon satin nan ne aka wayi gari da wani labari da ke cewa Firai Ministan Kasar Canada Justine Trudeau ya roki shugaba Buhari ya bai wa kasar sa yan cirani miliyan daya daga kasarnan. Labarin ya yadu sosai a shafukan sada zumunta da kafar Intanet.
Yan Najeriya sun fara tafka muhawa akan barin kasar da neman kasar da ya dace su koma bayan da hukumar Zabe ta INEC ta ta sanar da dage babban zaben shekarar 2019, kafin daga bisani a gudanar da shi.