Ko wane hali a ke ciki game da Dokar Mafi Ƙarancin Albashi?

160

A ranar Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu ga Dokar Mafi Ƙarancin Albashi (wadda aka yi wa kwaskwarima), wadda ta amince da N30,000 a matsayin mafi ƙarancin a abinda za a biya ma’aikaci a Najeriya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman Kan Harkokin Majalisar Dattijai, Ita Enang ya tabbatar da wannan ci gaba lokacin da yake yi wa manema labarai dake Fadar Gwamnati jawabi ranar Alhamis a Abuja.

A watan Janairu ne Shugaba Buhari ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta amince da N27,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, maimakon N30,000 da masu ruwa da tsaki suka amince da.

Mista Enang ya ce da wannan doka, ya zama wajibi ga masu kamfanoni su riƙa biyan ma’aikatansu N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan