Kotu ta soke zaɓen wani Sanata a Ebonyi

171

Wata Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi ta soke zaɓen Sonni Ogbuoji, Sanata mai wakiltar Mazaɓar Sanata ta Ebonyi ta Kudu, ta kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ta sake gudanar da sabon zaɓe a Mazaɓar ba tare da ɓata lokaci ba.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Akintola Aluko ya kuma umarci INEC da ta karɓe Takardar Shaidar Cin Zaɓe da ta ba Sanata Ogbuoji a shekara ta 2015 ba tare da ɓata lokaci ba, ta kuma gudanar da sabon zaɓe don cike gurbin kujerar.

Kotun ta yanke hukuncin cewa sakamakon canza sheƙa daga jam’iyyar da aka zaɓe shi zuwa wata, ya saɓa wa Sashi na 68 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar nan na shekarar 1999.

Alƙalin ya kuma umarci Sanatan da ya mayar da dukkan wasu kuɗaɗen da suka shafi albashi, alawus ko dukkan wani kuɗi da ya karɓa a matsayin Sanata tun daga lokacin da ya canza sheƙar zuwa lalitar gwamnati.

“Sashi na 68 (1) ya ce ɗan Majalisar Dattijai ko Majalisar Wakilai dole zai bar kujerarsa a Majalisar idan ya kasance mutumin da wata jam’iyyar siyasa ta ɗauki nauyinsa, ya zama mamba a wata jam’iyyar siyasar kafin wa’adin wannan Majalisar da aka zaɓe shi ya ƙare. Matuƙar dai shiga jam’iyyar sa ta biyu ba ya zo ne sakamakon ɓaraka a jam’iyyar da da yake mamba ba a da, ko kuma sakamakon haɗewar jam’iyya biyu ko fiye da haka, ko kuma akwai tsagi a ɗaya daga cikin jam’iyyun da ta ɗauki nauyinsa a baya.

“A wata ma’anar, duk wani ɗan Majalisar da ya koma wata jam’iyyar siyasa a lokacin da jam’iyyar da aka zaɓe shi ba ta fuskantar kowane irin rikici ko kuma ba haɗewa ta yi da jam’iyya biyu ko fiye da haka ba dole zai bar kujerarsa”, in ji Mai Shari’a Aluko.

Hukuncin dai ya biyo bayan wata ƙara mai lamba FHC/AI/CS/44/2018 da Evo Ogbonnaya Anegu, Oti Ama Ude, Uche Richard Ajali, Una Sunday Okoro da Simon Ajali Ogbadu suka shigar.

Masu ƙarar dai sun maka Sanata Ogbuoji ne a Kotu da INEC (wadda ake ƙara ta biyu), suna roƙon Kotun da ta bayyana kujerar Sanata Ogbuoji a matsayin wadda ba kowa a kanta sakamakon canza sheƙa zuwa jam’iyyar APC a lokacin da babu rikici ko rarrabuwar kawuna a jam’iyyar PDP.

Sun kuma roƙi Kotun da ta umarci wanda ake ƙara na farko (Ogbuoji) da ya mayar da dukkan kuɗaɗen da aka biya shi tun watan Janairun 2018 lokacin da ya canza sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar PDP.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan