Kotun Ɗa’ar Ma’aikata ta yanke wa Onnoghen hukunci

190

Kotun Ɗa’ar Ma’aikata, CCT ta yanke wa tsohon Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Walter Onnoghen hukunci sakamakon samun sa da laifin ƙin bayyana kadararsa lokacin da aka naɗa shi wancan muƙami.

A cewar hukuncin, Mista Onnoghen zai yi asarar dukkan kuɗaɗen dake cikin asusunsa na banki, kuma ba zai riƙe wani muƙamin gwamnati ba nan da tsawon shekaru goma.

Hukuncin ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya za ta mayar da dukkan kuɗaɗen dake asusun ajiyar Mista Onnoghen na banki mallakinta.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ce dai ta maka Mista Onnoghen a Kotu, sakamakon ƙin bayyana kadarorinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan