Rikicin Zamfara: An Kama Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma Da Hannu.

180

Rundunar Sojojin Operation Sharan Daji sun kama mataimakin shugaban karamar hukumar Anka da ke jihar Zamfara bisa zargin yana daa masaniya akan harkar ta’addanci a jihar.

Mai magana da yawun rundunar mista Clement Abiade ne ya bayyana haka ga manema labarai a garin Abuja. Ya ce an kama mutumin mai suna Yahuza Wuya bayan samun bayanai na sirri da ke nuna yana da hannun a aikin ta’addanci ga al’ummar Wuya da Sunke.

Mista Clement ya ce, mutumin yana taimakawa yan ta’addanvwajen siyar da shanaye da Jakunan da suka tare da gaya musu shirin Rundunar da na sauran jami’an tsaro har da na yan bijilanti. Haka zalika ya taimaka wajen kubutar da wani sanannen dan bindiga daga gidan yarin Gusau mai suna Sani Yaro.

Ya kara da cewa rundunar ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu masu kaiwa yan ta’adda bayani akan haryar Burukusuma zuwa Sabon Birnin a jihar Sokoto. Mutanen biyu masu suna Ibrahim Bangaje da Ado Bayero, za a mika su hannun jami’an tsari da zasu gudanar da bincike, kana a yanke musu hukunci.

Shugaban Rundunar Operation Yaki manjo Janar Hakeem Otiki ya tabbatar da kokarinsu wajen ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihohin Katsina, da Zamfara, da Sokoto, da Kebbi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan