Tsohon Shugaban Kasar Peru Ya Kashe Kansa

163

Tsohon shugaban kasar Peru Alan Garcia ya harbi kansa da bindiga a lokacin da Yan Sanda suka je kama shi.

BBC Hausa sun rawaito cewa ana zargin mista Garcia da karbar cin hancin daga wani kamfanin gine-gine na kasar Brazil mai suna Odebrecht.

Tsohon shugaban kasar ya sha musanta zargin karbar cin hanci kafin rasuwarsa. Da farko dai an aika Yan Sanda da su kama mista Garcia kan zarge-zargen da ake masa amma sai ya gwammace ya harbe kansa da ya yarda a kama shi. Daga bisani aka garzaya da shi asibiti kuma anan ne rai ya yi halinsa.

A baya-baya nan marigayin ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa yana fuskantar bita da kullin Siyasa ne, saboda babu wata shaida da ke nuna ya aikata laifin.

A watan Oktoban shekarar 2018, aka kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a a kasar ta Peru wadda ta nuna kashi 94 na al’ummar sun yi amannar cewa cin hanci da rashawa ya yi matukar kamari a kasar.

A yanzu haka ana tuhumar tsofaffin shugabannin kasar hudu akan badakalar cin hanci da rashawa da suka hadar da;

  1. Alrjandro Toledo- Ya yi mulkin kasar daga shekarar 2001 zuwa 2006 kuma ana zargin shi da karbar dalolin amurka daga kamfanin Odebrecht.
  2. Alan Garcia- Marigayi da ya harbe kansa ya mulki kasar a karo na farko daga shekarar 1985 zuwa 1990, sannan ya sake a karo na biyu daga shekarar 2006 zuwa 2011. Ana zarginsa da karbar na goro daga Kamfanin Odebreacht.
  3. Ollanta Humala- ya yi mulki daga shekarar 2011 zuwa 2016 kuma ana zarginsa da karbar cin hanci daga kamfanin Odebreacht.
  4. Pedri Pablo Kuczynski- ya yi mulki daga shekarar 2011 zuwa 2018 kuma ana zarginsa da badakalar sayen kuri’u. A makon da ya gabata aka tsare shi. Cikon na biyar dinsu shi ne Alberto Fujimori wanda ke gidan yari akan laifin cin hanci da cin zarafin dan Adam.

Shi dai kamfanin na Odebreacht kamfanin gine-gine ne na kasar Brazil wanda ya gina abubuwan more rayuwa dabam-dabam a fadin duniya. Masu bincike sun ce Kamfanin ya bai wa jami’ai da yan Siyasa cin hanci a matsayin toshiyar baki don samun kwangiloli masu tsoka. Kamfanin ya ce ya bada cin hanci a fiye da rabin kasashen yankin Latin Amurka da kuma Angola, da Mozambique a Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan