Shugaba Buhari Ya Taya Mabiya Addinin Kirista Murnar Bikin Easter

159

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk wata mai yiwuwa domin kawo karshen kashe-kashen da satar mutane da tashe-tashen hakula a kasarnan.

Shugaba Buhari ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke taya yan Najeriya mabiya Addinin kirista murnar bikin Easter. Sannan ya bukace su da suyi koyi da Yesu Al-masihu da kyawawan koyarwarsa akan kaunar juna, da yafiya, da tausayi, da juriya, da jarumtaka, da sadaukarwa.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa zata wadata jami’an tsaro da kayan aiki da goyon bayan magance aikin yan ta’adda, da barayi da masu garkuwa da mutane a kasarnan.

A sanarwan da ke dauke da sa hannun sa, shugaban kasar ya ce yana taya daukacin yan Najeriya baki-daya murnar bikin Easter wannan shekarar musamman mabiya addinin kirista . Ya kara da cewa a yanzu kasarmu tana fama da takaici bisa kashe-kashe, da satar mutane, da fadace-fadace a jihohin kasarnan.

Don haka, shugaban ya ce wannan lokaci ne da zamu kara dankon yan’uwanta ka da ke tsakaninmu, da mutunta makotaka, kada mu bari bambancin da ke tsakaninmu ya zama sanadiyyar rashin zaman lafiyarmu.

Shugaba Buhari ya ce babban abin ya ke wajibi ga gwamnatinsa shi ne ya samar da shugabanni jajirtattu masu gaskiya, sannan yan kasa su samu kwanciyar hankali, su yi kasuwanci da sauran hidimomin rayuwa, sannan ma’aikatan gwamnati su kasance masu rikon amana, sai Fannin shari’a su hukunta masu karya dokar kasa.

A karshe , shugaba Buhari ya yi kira ga daukacin yan Najeriya da su karfafa Addu’ar zaman lafiya, da tsaro a kasarnan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan