Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ya bayyana wata babbar masifa dake fuskantar ƙasar nan

183

Sonny Echono, Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ya ce kusan ‘yan Najeriya miliyan 60 ne ba su iya rubutu da karatu ba, yana mai tabbatar da cewa Cibiyoyin Karatu za su yi maganin matsalar rashin iya rubutu da karatun a ƙasar nan.

Mista Echono ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Otobi, a Jihar Benue yayin ƙaddamar da Cibiyar Karatu ta Gwaji ta Shiyyar Siyasa ta Arewa ta Tsakiya.

Babban Sakataren ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa yadda matsalar rashin iya rubutu da karatu tsakanin matasa da dattawa ta yi yawa, yana mai nanata cewa matakin iya rubutu da karatu a tsakanin ƙananan ma’aikatan Kwalejin shi ma abin damuwa ne.

Mista Echono ya ce Cibiyoyin Karatu da za a buɗe a dukkan Kwalejojin Gwamnatin Tarayya guda 104 dake ƙasar nan za su rage matsalar rashin iya rubutu da karatu tsakanin ƙananan ma’aikatan makarantun, yana mai nanata cewa Gwamnatin Tarayya ta tsara shirin ne musamman don su da kuma al’umomin dake kusa da makarantun.

Ya ce iya rubutu da karatu abu ne da ya shafi zamantakewa da haƙƙin ɗan Adam, ya kuma yi kira ga ɗalibai da suke a Cibiyar Karatun ta Gwaji da su jajirce, su kuma ɗauki karatunsu da muhimmancin gaske.

Ya ce manufar shirin shi ne don ya dace da Shirin Muradun Ƙarni, musamman abu na huɗu a cikin Shirin wanda ya buƙaci a ba kowa da kowa ilimi mai inganci.

Ya ce shirin zai ba waɗanda za su amfana dabarun iya rubutu da karatu da kuma iya dabarar gane lambobi don ba su damar fuskantar ƙalubalen rayuwa.

Wani jami’i daga Ofishin Mataimaki na Musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari Kan Muradun Ƙarni, SDG, Stephen Ojo ya yaba wa hangen nesa na Gwamnatin Tarayya wajen tsara wannan shiri, ya kuma yi alƙawarin tallafa wa shirin don samun nasararsa.

Shugaban Makarantar, Amudipe Gabriel ya yaba wa Babban Sakataren sakamakon tsayuwar daka da ya yi wajen tabbatar da cewa an fara shirin da wuri, da kuma yadda ya mayar da Makarantar Cibiyar Shirin a yankin.

Mai kula da shirin, Abisode Olayiwola, a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ce yadda ɗalibai a makarantar da al’umomin dake kusa suka karɓi shirin ya wuce kayan aikin da aka tanada.

“Mun yi tanadin ɗalibai 40 ne, amma abinda muke da shi ya ninka wannan adadi, yadda mutane suka fito sosai abin ya birge mu. Za mu yi musu shiri na musamman gaba ɗayansu”, in ji Mista Olayiwola.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan