Firai Ministan Kasar Mali Da Gwamnatinsa Sun Yi Murabus Bayan Kashe Fulani 160

205

Firai Mininstan Kasar Mali da gwamnatinsa baki daya sunyi murabu, biyo bayan kwashe mako hudu da kashe wasu makiyaya sama da mutum 160 a wani hari da yan bindiga suka kai wani kauye.

BBC Hausa sun rawaito cewa Yan bindigar sun kai hari kan kauyen Ogossagou da ke tsakiyar kasar Mali, tun a watan Maris kuma harin ya girgiza kasar sosai.

Rahotanni sun ce harin da aka kai kan fulani makiyaya wanda ake zargin mafarauta ne suka kai daga yankin Dogon, shi ne mafi muni a tarihin rikicin kasar. Hakan ya sa shugaban gwamnatin kasar da ministocinsa yin murabus a jiya alhamis, 18 ga watan Afrilu.

A ranar laraba, 17 ga watan Afrilu ne majalisar dokokin kasar Mali ta soma tattaunawa batun jefa kuri’ar tsige Firai Mininsta Soumeylou Boubeye Maiga bisa gazawar gwamnatinsa na karba makamai daga hannun kungiyoyin yan bindiga na sa-kai, tare da murkushe mayaka masu ikirarin jihadi.

BBC Hausa sun kara da cewa Shugaban Kasar Ibrahim Boubacar Keita, a wata sanarwa ya ce, ya amince da murabus din firai ministan da ministocinsa.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za a nada sabon firai minista tare da kafa sabuwar gwamnati bayan tattaunawa da dukkan bangarorin siyasa.

A farkon watan nan ne dai aka yi gagarumar zanga-zanga a kasar Mali inda aka yi kira ga gwamnati da ta tashi tsaye, ta kara kaimi domib magance rikici tsakanin kabilu da ke gaba da juna, wanda ya raba dubban jama’a da muhalli.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan