Jami’ar Jihar Akwa Ibom za ta kori wasu ɗalibai huɗu

63

Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Jihar Akwa Ibom ta ce za ta kore wasu ɗalibai huɗu masu karatun digiri na farko sakamakon zargin su da hannu wajen yi wa wata ɗaliba fyaɗe a Harabar Jami’ar dake Obio Akpa a yankin Ƙaramar Hukumar Oruk-Anam.

Shugaban Sashin Yaɗa Labarai, Huɗɗa da Jama’a da Tsarin Muƙamin Jami’ar, Mista Akaninyene Ibanga ya bayyana haka ga manema labarai ranar Juma’a a Oruk-Anam.

Mista Ibanga ya ce Jami’ar za ta kori ɗaliban daidai da yadda sakamakon binciken ‘yan sanda zai nuna.

Ya ce ‘yan sanda ba za su sake su ba don kuwa tuni wadda aka yi wa fyaɗen ta samu rahoton likitoci don ƙarfafa binciken nasu.

Da farko hukumomin Jami’ar sun dakatar da ɗaliban a matsayin wata ƙa’ida da aka saba da ita don ba su damar halartar tattaunawa da ‘yan sanda a matsayin ɓangaren binciki don tabbatar da yadda suke da hannu a laifin.

“Ba yadda za a yi ‘yan sanda su sake saboda wadda aka yi wa fyaɗen ta samu wani rahoton likitoci don ƙarfafa binciken ‘yan sanda.

“Da zarar ‘yan sanda sun kammala bincikensu sun aiko da rahoto, Jami’ar za ta kore su”, in ji Mista Ibanga.

Ɗaliban da ake zargi da yin fyaɗen su ne Akpan Matthew, Essien Fidelis, Bassey Joseph da Bassey Columbus.

“Ku sani cewa Shugaban Jami’ar Jihar Akwa Ibom ya ɗauki matakan ladabtarwa da suka dace a kan ɗalibai guda huɗu waɗanda ake zargin da laifin yin fyaɗe kwanan nan, waɗanda suka kunyata al’ummar Jami’ar”, in ji shi.

A cewarsa, Shugaban Jami’ar ya umarci Magatakarda kuma Sakataren Majalisar Dattijai ta Jami’ar, Mista John Udo da ya ba ɗaliban masu laifi wasiƙa tun ranar 8 ga watan Afrilu.

Ya ce ranar 23 ga watan Maris Jami’ar ta samu rahoton jami’an tsaro dake cewa wasu ɗalibai guda huɗu sun yi wa wata ɗalibai dake Sashin Nazarin Aikin Jarida fyaɗe, sun kuma ji mata ciwuka a jikinta.

Mista Ibanga ya bayyana cewa an ba ɗaliban wasiƙar dakatarwa ne kamar yadda dokoki da ƙa’idojin Jami’ar suka tanada, kuma suke ƙunshe a cikin Littafin Bayanai na Ɗalibai.

Ya ce Shugaban Jami’ar ya bada umarni a madadin Majalisar Dattijan Jami’ar da a dakatar da ɗalibtar masu laifin su huɗu, sakamakon rashin ɗa’a, abinda ya saɓa da rantsuwa da suka ɗauka, kuma dakatarwar ta fara aiki ne tun daga ranar da aka rubuta wasiƙun.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan