Mutum Biyu Sun Rasa Rayukansu Sanadin Zaftarewan Kasa A Jigawa

36

Rundunar Yan Sanda jihar Jigawa ta bayyana cewa wasu matasa biyu sun rasa rayukansu sanadiyyar zaftarewan kasa a kauyen Bakin-Jeji da ke karamar hukumar Dutse.

Mai magana da yawun rundunar S.P Audu Jinjiri ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

S.P Audu Jinjiri ya ce zaftarewan kasar ya faru a ranar laraba da misalin karfe 1:30 na rana kuma ya rutsa da matasan biyu watau Alkassim Auwalu mai shekaru 16, da Tahir Rilwanu mai shekaru 12. Labarin faruwar lamarin ya iso ga rundunar yan Sanda da misalin karfe biyu na rana.

Ya kara da cewa, lamarin ya faru a lokacin da matasan biyu ke hakan rami. Kwatsam sai kasan ya zaftare ya binne su, kuma a nan ta ke suka rasa rayukansu.
Rundunar Yan Sandan ta garzaya da matasan biyu ziwa asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu. Daga nan an mika wa dangin matasan gawawwakin domin jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
S.P Jinjiri ya ce duk da haka za a cigaba da bincike akan lamarin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan