An kama ɗalibai da dama sakamakon maguɗin jarrabawa- JAMB

232

Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 100 masu maguɗin jarrabawa a faɗin ƙasar nan a Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Bai Ɗaya, UTME da aka kammala kwanan nan, a cewar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB.

A Jaridarta ta Mako-mako da Mai Magana da Yawun Hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar ranar Litinin a Abuja, JAMB ta ce an samu waɗannan ɗalibai ‘yan damfara ne da hannu wajen yin rijista fiye da sau ɗaya don su samu sauƙin yin sojan gona a lokacin da ake tsaka da gudanar da jarrabawar.

Hukumar ta lura da cewa hakan yana ɗaga yawan rijistar Jarrabawar ta UTME da ake duk shekara da kaso 30 cikin ɗari.

JAMB ta ce bayanan da take da su sun nuna cewa ana yin wannan mummunar ɗabi’a kusan a dukkan jihohin ƙasar nan, har da Abuja.

Daga cikin mutanen da aka cafke akwai wani shahararren mai maguɗin jarrabawa wanda ya yi rijista sau 60 don ya yi maguɗi ya rubutawa ɗalibai 60 jarrabawar.

Hukumar ta ce an iya kama masu laifin ne sakamakon binciken ƙwaƙwaf kuma na wajibi da take yi wa waɗanda za su zana jarrabawar, don fito da ƙwararrun masu maguɗin jarrabawa kafin sakin sakamako.

JAMB ta ce ta soke sakamakon Cibiyoyin Ɗaukar Jarrabawa ta Kwamfuta, CBT guda biyu a Abia a wani abinda ta bayyana da ‘yawaitar rashin bin ƙa’ida lokacin da ake tsaka da zana UTMEn’.

Hukumar ta ce cibiyoyin biyu su ne Heritage and Infinite CBT Centre da Okwyzil Computer Institute Comprehensive School, Ugwunabo, Aba, Abia.

Ta ce ya zama wajibi ta ɗauki wannan mataki sakamakon hujjoji da ta samu daga Na’urorin Ɗaukar Hoto na CCTV da ƙwararrun ma’aikata da Hukumar ta ɗauka suka ba ta.

“To, amma don kar a hukunta ɗalibai masu gaskiya masu aiki tuƙuru waɗanda suka samu kansu a waɗannan cibiyoyi biyu, Hukumar ta canza wa dukkan ɗaliban da suka zana jarrabawa ko aka shirya za su zana jarrabawa a cibiyoyin biyu zuwa wasu cibiyoyin inda daga bisani suka zana jarabawar tasu”, in ji ta.

To amma JAMB ta nemi afuwar ɗaliban da ba su ji ba ba su gani ba waɗanda aka canza wa wuraren zana jarrabawar bisa rashin jin daɗi da hakan zai iya jawo musu, tana mai tabbatar da shirinta na bada dama ta bai ɗaya ga dukkan ɗalibai don cimma gurinsu.

Hukumar ta ce ta soke dukkan sakamakon jarrabawar da ta gudanar a cibiyoyin biyu daga 11 zuwa 18 ga watan Afrilu

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan