Ko mene ne gaskiyar zargin da ake yi wa JAMB cewa tana rage wa ɗalibai maki?

58

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB ta ce rahoton da ake yaɗawa cewa Hukumar na rage makin ɗaliban da suka zana Jarabawar Bai Ɗaya ta Shiga Manyan Makarantu, UTME ƙarya ne.

A wata sanarwa da Shugaban Sashin Yaɗa Labarai na Hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai ranar Litinin a Abuja, Hukumar ta ce rahoton ƙarya ne.

Rahoton ya yi ikirarin cewa Hukumar na rage wa ɗalibai da suka zana Jarabawar ta UTME, waɗanda aka samu da maguɗin jarrbawa maki 100 kowane.

JAMB ta ce wani bincike da ta gudanar ya nuna cewa wasu gungun ɓata gari ne dake zaune a wani gari, Igarra dake jihar Edo suka kitsa labarin na ƙarya.

Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin damfara, kuma an haɗa shi ne don a tatsi iyaye.

“Wani gungun ɓata gari da suka fito daga wani gari da ake kira Igarra dake Jihar Edo, kuma suke da mambobi a jihohin Lagos, Ogun, Osun, Abia, Anambra da Plateau suna yaɗa sanarwar ƙarya na rage wa ɗalibai makin UTME.

“Wannan an yi ne da niyyar a cuci iyaye da ɗalibai.

“Ɗalibai za su samu sakamakonsu ta wayoyin da suka yi rijista da zarar an kammala tantance cibiyoyin jarrabawar, za a kuma a bayyana wa jama’a.

“Ɗaliban da iyayen da za a damfara ne kaɗai wannan labarin ƙanzon kurege zai yi wa illa”, in ji Hukumar.

A ranar Lahadi, Mista Benjamin ya gargaɗi ɗalibai da kada a yaudare su da jita-jita da sanarwar ƙarya da ake yaɗawa a wasu kafafen watsa labarai, musamman kafafen sada zumunta na zamani.

Ya kuma ce Hukumar ta nesanta kanta da jita-jitar sakin sakamakon jarrabawar UTME da aka kammala kwanan nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa JAMB ta gudanar da Jarrabawar UTME ne daga 11 zuwa 18 ga watan Afrilu.

Kusan ɗalibai miliyan biyu ne suka yi rijistar jarrabawar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan