Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Harin Kasar Sri Lanka Yayin Bikin Easter

303

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da akai kai coci-coci da kuma otel ranar lahadi, 21 ga watan Afrilu wanda ya kasance ranar bikin Easter a kasar Sri Lanka.

Shugaban kasan ya bayyana rashin jin dadinsa ne ta hannun mataimakinsa na musamman akan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.

A wani sako da ya wallata a shafinsa na twitter, Malam Garba Shehu yace, “amadadin gwamnatin kasarnan da mutanen ta, shugaban kasa na ta’aziyya ga iyalen wanda aka kashe a lokacin harin kuma yana fatan samun sauki ga wanda suka samu raunuka”.

Mummunan harin da aka kai, yayi sanadiyyar mutuwar kusan mutum 300, sannan kuma ya raunata sama da mutum 500 a lokacin da ake tsaka da gudanar da bikin easter a kasar sri lanka.

Hankalin kasashen duniya baki daya ya tattara kan hare-haren da aka kai kasar Sri Lanka, ganin irin asarar rayuka da dukiyoyi da akayi a lokaci kankani kuma ana zargin yan kunar-bakin wake ne suka kai.

Shugabanin Kasashen Amurka da Ingila sun bayyana alhininsu, tare da yin Allah wadai akan faruwar Lamarin a shafukansu na Twitter.

Sauran shugabanin kasashen duniya da dama na cigaba da nuna alhininsu tare da yin ta’aziyya ga kasar ta sri lanka, sannan kuma sunayin ALLAH wadai da hare haren da aka ka

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan