Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuma jam’iyyar ta PDP sun bayyana cewa Atiku cikakken ɗan Najeriya ne domin kuwa iyayensa suna da asali a Arewa Maso Yamma, don haka ya cancanci ya yi takarar shugabancin ƙasar nan.
Atiku da jam’iyyar PDP sun mayar da martani ne ga ikirarin da jam’iyyar APC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari suka yi a gaban Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa dake zama a Kotun Ɗaukaka Ƙara ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu, 2019.
Jam’iyyar APC ta bayyana a ikirarin da ta yi cewa Atiku ɗan Kamaru ne, saboda haka bai cancanta ya yi takarar shugaban ƙasa ba bisa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
To, amma a martanin da lauyoyin Atiku bisa jogorancin shugabansu, Livi Uzoukwu, suka yi, ya ce mahaifinsa, Garba Abubakar haifaffen ɗan Najeriya ne da aka haifa a Wurno dake jihar Sokoto a halin yanzu, yayinda mahaifiyarsa, Aisha Kande ita ma ‘yar Najeriya ce da aka haife ta a Dutse dake jihar Jigawa a halin yanzu.
Ya ce dukkaninsu ƙabilar Fulani ne, ‘yan asalin Najeriya.