Home / Gwamnati / ASUU Ta Yi Suka Ga Yunkurin Kafa Jami’a Da Sunan Shugaban Kasa.

ASUU Ta Yi Suka Ga Yunkurin Kafa Jami’a Da Sunan Shugaban Kasa.

Kungiyar Malaman Jami’o’i na Kasa (ASUU) ta soki shirin uwargidan Shugaban kasa Muhammad Buhari na bude jami’a da sunansa.

Kungiyar ta yi Allah wadai da wannan shiri inda ta ce batutuwan mai dakin shugaban kasar ya yi kama da wasan yara.

A wani tattaunawa da manema labari a lokuta dabam-dabam, shugaban kungiyar ASUU reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Deji Omoli da Tsohon ma’ajin kungiyar ASUU na Kasa, Farfesa Ademola Aremu sun soki shirin a garin Ibadan.

Farfesa Omole ya ce a lokacin da ya samu labarin za a gina jami’a mai zaman kanta, mai dauke da sunan shugaban kasa a matsayin wani abun wasa. Abin takaici ne a ce shugaban kasa ya kasa daukan nauyin jami’o’in gwamnati amma mai dakinsa zata bude jami’a mai zaman kanta da hadin gwiwar turawa. Wannan ya nuna wa yan Najeriya cewa ba bunkasa Ilimin makarantun gwamnati ne a gaban gwamnatin Buhari ba.

Don haka, ya ce ya zama wajibi mu tabbatar wa gwamnatin tarayya matsayin daukaka fannin Ilimi da muhimmancin sa, wanda da shi ne kadai zamu samu cigaban da ya da ce.

A nasa bangaren, Farfesa Aremu ya bawa haj. Aisha Buhari shawara inda ya ce, kamata ya yi ta nusar da shugaban kasar muhimmancin ilimi da kuma fitar da manufofi da zasu daukaka fannin Ilimi. Mista Aremu ya bada misali cewa a baya tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bude jami’a mai zaman kanta na Bell, yin hakan yasa suka yi Allah wadai da abin da ya yi, sannan mataimakinsa Atiku, shi ma ya bude nashi, nan ma mun nuna bacin rai. Don haka duk mai son kafa wani abu ko sana’a, to kada mutum ya rike mukamin gwamnati, ya bar ma masu kishin al’umma su rike domin yi wa jama’a aiki.

Ya kara da cewa a kasarnan mutum nawa ne zasu iya biyawa ýaýansu kudin karatun a jami’o’i masu zaman kansu. Don haka idan har da gaske haj. Aisha ta ke kan batun gyara fannin Ilimi, to ta taimaka a inganta jami’o’in da muke da su. Idan kuma tana so ta bide jami’a mai zaman kanta ne, to ta bari sai sun sauka daga gwamnati, ba yanzu da suke rike da ragamar mulki ba.

A farkon satin nan ne, mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta bayyana niyyar ta na kafa jami’a mai zaman kanta a jihar Adamawa ta hadin gwiwar Turawa domin taimakawa fannin Ilimi a Kasarnan.

About Amina Hamisu Isa

Check Also

Bayan Kwashe shekaru 27 a ƙarshe Bill Gates ya saki matarsa Melinda

Bill Gates, wanda da shi aka kirkiri kamfanin Microsoft, da matarsa, sun amince za su …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *