PDP ta dakatar da Shugaba da Mataimakinsa

178

Jam’iyyar PDP, Reshen Jihar Plateau ta zartar da ƙuri’ar yanke ƙauna ga Shugabanta na Jihar, Damishigi Sango da Mataimakinsa, Amos Gambi.

Majalisar Zartarwa ta Jam’iyyar ce ta yanke hukuncin korar jami’an “don tseratar da jam’iyyar” a wani taron tattaunawa da ta yi ranar Laraba da sassafe a Jos, babban birnin jihar.

Majalisar Zartarwar, wadda mambobi 16 suka sa hannu a matakin korar jami’an da ta ɗauka, ta naɗa Chris Hassan, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar a Mazaɓar Sanata ta Arewa a Jihar a matsayin Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN jam’iyyar PDP ta kira taron ne don tattauna batutuwan da suka taso daga zaɓe, daga nan kuma aka amince da dakatar da jami’an biyu bisa zargin su da kashe kuɗaɗen da aka tura wa jam’iyyar na zaɓen shugaban ƙasa ba bisa ka’ida ba.

Jam’iyyar ta kuma zargi jami’an biyu da kasa yin bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ware don tallafa wa ‘yan gudun hijira, IDPs.

Da yake mayar da martani, Mista Sango ya ce bai san da waccan kora ba.

“Ba wanda ya faɗa min wani abu. Ban sani ba. Ba wanda ya fuskance ni da wani zargi.

“Maƙiya ne dake ƙoƙarin rusa jam’iyyar. Akwai wasu mutane da suka fusata bisa wasu dalilai. Suna son su rusa jam’iyyar. Amma, zan yi maganin su. Zan yi maganinsu”, Mista Sango ya shaida wa NAN haka a wata tattaunawa ta waya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan