Wani ɗan Majalisa ya ba Buhari shawarar inda ya kamata ya zaɓo Sakataren Gwamnatin Tarayya

155

Wani ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Anambra, Tony Nwoye ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari da ya zaɓo Sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF daga Kudu Maso Gabashin ƙasar nan.

Mista Tony wanda ke wakiltar Mazaɓar ɗan Majalisar Tarayya ta Anambra ta Gabas da ta Yamma ya bada wannan shawarar ne yayin wani bikin shirin bada tallafi a Nsugbe dake kusa da Onitsha ranar Laraba.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samun karɓuwar jam’iyyar APC a yankin.

“Mutanenmu suna jin cewa an mayar da su saniyar ware.

“Inyamurai suna da matuƙar muhimmanci ga Najeriya. Bai kamata a mayar da mu saniyar ware ba kawai don ba mu zaɓi Buhari ba.

“Yankin Kudu Maso Gabas ya cancanci samun muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya ko Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai”, in ji ɗan Majalisar.

“Shugaban Ƙasa, kasancewar sa mai faffaɗar zuciya, ya kamata ya ba Inyamurai damar su ji cewa lallai su ma ana yi da su, ya sa su ji cewa su ma wani ɓangare ne na Najeriya”, in ji Mista Nwoye.

Ya ƙara da cewa yin naɗin zai taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar APC yadda za ta iya cin zaɓuka na gaba a yankin.

Ya yabi Gwamnatin Tarayya bisa gina hanyoyi huɗu a mazaɓar tasa, da kuma bayar da kwangilar gina wata hanyar bisa tsabar kuɗin N320m.

Mista Nwoye ya ce kwanan nan za a fara aiki a hanyar Anambra-Kogi-Abuja.

“Na samu tabbas daga Gwamnatin Tarayya cewa aikin wanda zai haɗa da gadoji bakwai kwanan za a bada umarnin fara shi.

Ya kuma bayyana ƙarfin guiwa cewa Gwamnatin Tarayya za ta kammala dukkan ayyukan da ake ci gaba da yi a yankin, ayyukan da suka haɗa da Gadan Naija ta Biyu

Game da shirin bada tallafin, ɗan Majalisar ya ce shirin wani ɓangare ne na inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa.

Rahotanni sun ce mutum 520 ne suka karɓi tallafin kuɗi daga N30,000 zuwa N100,000 don su fara sana’a ko kuma su ƙara jari.

Ɗan Majalisar ya kuma raba babura 120, injinan ɗinki 55, jannareto 50 da injinan markaɗe guda 50.

Tun da farko, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Anambra, Basil Ejidike ya ce raba tallafin da Mista Nwoye ya yi ya yi daidai da manufofin jam’iyyar APC na kakkaɓe talauci.

Mista Ejidike wanda ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su yi koyi da abin kirkin, ya ce jam’iyyar ba za ta yi sako-sako ba wajen sasanta mambobinta da aka ɓata wa a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan