Buhari zai je Birtaniya

151

Bayan ziyarar aiki da ya kai Jihar Lagos ranar Laraba, Shugaba Muhammadu Buhari zai je ziyarar ƙashin kai Birtaniya ranar Alhamis.

Femi Adesina, mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Kafafen Watsa Labarai ya bayyana haka a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.

“Bayan ziyarar aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai Jihar Lagos ranar Laraba inda ya ƙaddamar da ayyukan ci gaba da dama da Gwamnatin Jihar ta gudanar, Shugaba ya shirya zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno don kai wata ziyarar aikin ranar Alhamis.

“Ana sa ran zai ƙaddamar da ayyukan ci gaba, musamman a ɓangarorin ilimi, lafiya da hanyoyi.

“A ƙarshen ziyarar, Shugaban Buhari zai wuce Birtaniya domin ziyarar ƙashin kai.

“Ana sa ran zai dawo Najeriya ranar 5 ga watan Mayu, 2019”, in ji Mista Adesina.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan