Sadaukarwa: Mai gadi ya zaɓi a gina burtsatse a garinsu a kan a gina masa gida

41

Wani mai gadi ya yi watsi da tayin gina masa gida a matsayin kyautar jin daɗi daga shugabansa, maimakon haka, sai ya ce a gina fanfon burtsatse a ƙauyensu, wanda ya ce ba su da ruwa.

Musa Usman, mazaunin Giljimmi ne, wata rugar Fulani dake Ƙaramar Hukumar Birniwa a Jihar Jigawa, yana kuma zaune ne a gidan kara.

Usman, wanda ya yi wa wani ɗan India, Mista V. Vergehese, Manajan Daraktan wani kamfanin magani a Lagos aiki tsawon shekara 25, ya bar aikin don ya dawo gida ya haɗu da iyalinsa.

Lokacin da Usman zai tafi, sai Mista Vergehese ya yi tayin gina masa gida don nuna jin zamansa da shi lokacin da yake yi masa gadi

Al’ummar ƙauyen da Usman sun kasance suna tafiya mai tsawo kafin su samu ruwan sha.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da burtsatsen,, ya ce ya yanke shawarar gina burtsatsen ne bisa tsantsar gaskiya da Usman ya nuna lokacin da yake aiki tare da shi.

“Usman ya yi min aiki cikin gaskiya tsawon shekara 25. Mukan tafi India mu bar gidanmu ƙarƙashin kulawarsa, kuma duk da haka, za mu samu komai yadda yake. Haƙiƙa, shi ɗan Najeriya ne mai gaskiya”, in ji Mista Vergehese.

Usman ya gode wa Mista Vergehese bisa wannan abin kirki, yana mai cewa bai yi da-na-sanin maye gurbin tayin gidan da gina wa al’ummar ƙauyen burtsatse ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan