Yau Ake Bikin Ranar Maleriya Ta Duniya

215


A ranar 25 ga watan Afrilun kowacce shekara ake bikin ranar Maleriya ta duniya. A rana irin ta yau ana bikin zazzabin cizon sauro domin samo hanyoyin kawar da cutar. Zazzabin cizon sauro wadda akan iya kare ta, kuma a warke idan har mutum ya kamu. Maleriya na daya daga cikin cututtuka masu kashe dubunnen mutane.

Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a duk minti biyu, cutar maleriya na kashe yaro guda, kuma a duk shekara ana ba da rahoton fiye da mutum miliyan 200 da suke kamuwa da cutar.

BBB Hausa sun lissafo abubuwan da ake bukata mutum ya sani ga me da cutar maleriya kamar haka;

  1. Maleriya cuta ne da ke barazana ga rayuka wadda wasu nau’o’in kwayar cuta hudu da ke yaduwa.
  2. Mutane na kamuwa da kwayar cutar ta hanyar cizon macen sauro.
  3. Ana iya kare kai daga kamuwa kuma ana warkewa.
  4. A shekarar 2017, an kiyasta samun mutum miliyan 219 da suka kamu da maleriya a kasashe guda 87. (WHO)
  5. Kuma anyi kiyasin mutuwar mutum 435,000 sakamakon cutar a shekarar 2017.
  6. Afirka ce ta fi fama da yawan masu kamuwa da cutar a fadin duniya. A shekarar 2017, nahiyar ta yi fama da kashi 92% na masu fama da maleriya, da kuma kashi 93% na mace-macen maleriya.
  7. Yawan kudin da ake samarwa don takaitawa da dakile cutar maleriya ya kai kiyasin dala biliyan 3.1 a shekarar 2017.

Bugu da kari, a shekarar 2017, kusan rabin al’ummar duniya ne suka fada cikin kasadar cutar maleriya. Kananan yara yan kasa da shekaru biyar sun fi zama cikin rukunin mutane da suka fi sauran kamuwa da cutar. Yara na da kashi 61% watau 266,00 na dukkan mace-macen da aka samu sakamakon cutar maleriya a duniya.

Haka nan, akwau hasashen cewa sauran rukunin al’umma kamar mata masu juna biyu da mutane masu rarraunar garkuwar jiki na fuskantar gagarumar kasadar kamuwa da cutar maleriya.

Alkaluman hukumar lafiya ta Duniya sun nuna cewa a shekara ta 2017, a cikin kasashe guda biyar ne aka samu kusan yawan adadin mutanen da suka kamu da cutar maleriya na fadin duniya kamar haka; Najeriya kashi 25%, sai Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kongo kashi 11%, sai Mozambique kashi 5%, India kashi 4%, sai Uganda kashi 4%.

Hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar amfani da hanyoyi guda biyu da ta tabbatar da ingancinsu domin samun kariya daga cutar Maleriya. Hanyoyin su ne amfani da gidan sauro, sai kuma fesa maganin sauro a cikin daki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan