Zaftarewar Kasa Da Ambaliyar Ruwa Ya kashe Mutane 60 A Afirka Ta Kudu

192

Kasar Afirka ta Kudu ta fuskanci ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Birnin Durban da kuma Yankin KwaZulu-Natal, wanda akalla ya yi sanadin mutuwar mutum 60.

Hakan ya faru sanadiyyar kwanaki da aka shafe ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankunan kudanci da gabashin kasar. Daga cikin wanda suka rasa rayukansu akwau jariri dan wata shida da wani karamin yaro.

BBC Hausa sun rawaiti cewa shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ziyarci yankunan da ambaliyar ta shafa kuma ya ce ambaliyar ta shafi fiye da mutum dubu daya wanda suka rasa muhallansu.

Bugu da kari, an yi hasashen cigaba da samun ambaliyar da iska mai karfin gaske a yankunan da ke gabar ruwa, don haka ana gargadib mutane su kula.

Ambaliyar ruwan ya kassata kasuwanci, da gidaje da lalata jami’o’i akalla biyu. Mutane da dama sun rasa muhallansu. Shugaba Cyril Ramaphosa ya mika ta’aziyyarsa ga yan uwab wanda suka mutu a iftila’in inda ya ce sun yi takaicin faruwar lamari domin irin wannan mutuwa akwai kaduwa musamman yadda ya faru a bazata.

Kafin ya kai ziyara yankunan da lamarin ya shafa, shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa da ya ce, “wannan yanayi da ake ciki na bukatar kowanne bangare ya yi aiki tukuru domin kaiwa wanda ambaliyar ta shafa tallafi”.

Mutane da dama ne aka kai asibiti kuma tawagar masu bincike da aikin ceto na cigaba da laluben gano wadanda suke da sauran rai ko baraguzan gini suka danne.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan