Asibitin Koyarwa A Jihar Sokoto Sun Fara Aikin Zuciya

222

Asibitin Koyarwa na Usmanu Dan Fodio da ke jihar Sokoto sun kaddamar da Fara gudanar da aikin tiyatar Zuciya. Shugaban asibitin Dr Nasir Muhammad ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin sokoto.

Dr Nasir ya ce mutane sama da 5,000 a cikin kowanni mutum miliyan daya da ke zaune a jihohin Sokoto, da Zamfara, da Kebbi ke bukatar aikin zuciya wanda dayawa daga cikin su basu da karfin da zasu iya biyan kudin aikin.

Ya kara da cewa, hakan yasa suka ga ya da ce su fara gudanar da wannan aiki don taimakawa al’umma. Don haka, ya yi kira ga gwambati, da Kungiyoyi, da masu kudi domin su kawo agaji ga shirin asibitin saboda yin aikin yana da tsadar gaske.

Asibitin koyarwan na Jihar Sokoto, a yanzu ya shirya yiwa iyakacin mutane Goma aiki kuma asibitin na da niyyar kaddamar da kungiyar tallafi ga al’umma masu bukatar aikin zuciya da basu da karfin biya. Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa aikin zuciya cikin shirin tallafinta na NHIS.

A yanzu haka, Asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio suna gudanar da aikin zuciyar ne da hadin gwiwar asibitin koyarwa na Sarki Muhammad na Shida da ke kasar Morocco a matsayin wata yarjejeniyar fahimtar juna da suka sa hannu.

Hadin gwiwar ya taimaka wajen koyar da ma’aikatan lafiya dabarun aiki da kuma yadda zasu yi amfani da kayan aiki na zamani wajen gudanar da aiki akan marasa lafiya.

A nashi bangaren, babban likitan tiyata na zuciya a jami’ar Usmanu Danfodio ya ce zuwa yanzu anyi wa marasa lafiya masu matsalar zuciya har mutum biyar aiki a kyauta tun lokacin da aka kaddamar da shirin. A yanzu haka asibitin na karbar naira miliyan biyu a matsayin kudin aikin.

Daga karshe, shugaban tawagar likitoci daga kasar Morocco, Farfesa Boumzevra Drissi, babban likitan zuciya ya ce ciwon zuciya na daya daga cikin ciwuka da ke kashe mutane a duniya. Don haka ya ja hankalin al’umma da su lura da abincin da suke ci kuma su guji shan taba sigari saboda hakan na janyo ciwon zuciya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan