Gwamnati Bata Yi Karin Kudi Ga Masu Yiwa Kasa Hidima Ba Inji Hukumar NYSC

200

Hukumar Matasa masu yiwa kasa hidima watau NYSC ta karyata jita-jita da ke yawo a kafofin sadarwa da ke cewa an yi karin kudin yan yiwa kasa hidima daga naira 19,800 zuwa 31,800 bayan da shugaban kasa ya sanya hannu a dokar karawa ma’aikata kudi a kasar nan.

Mataimakin Daraktan hukumar na kasa, mista Eddy Megwabne ya bayyanawa manema labarai hakan ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu inda ya ce gwamnatin tarayya bata sanar da su shirin karawa yan yiwa kasa hidima kudi ba.

Ya kara da cewa duk da ya ke ba hukumar NYSC ce ke biyan yan yiwa hidiman kudi ba, amma ya san gwaamnatin tarayya zata sanar da du idan ma akwai shirin karin kudin kuma duk halin da ake ciki.

Don haka, mista Eddy ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa a kafafen sadarwa. Idan gwamnatin Tarayya ta shirya kara albashi, za ta sanar da Hukumar NYSC su kuma za su sanar da al’umma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan