Gwamnatin Jihar Kano za ta shigo da bas-bas na zamani

342
PIC.28. SOME OF THE 100 AIR CONDITIONED LAGBUS BUSES INAUGURATED BY GOV. FASHOLA OF LAGOS IN LAGOS ON TUESDAY (17/2/15) 908/17/2/15/MA/AIN/NAN

Gwamnatin Jihar Kano ta sa hannu a kan wata Yarjejeniya Fahimtar Juna, MoU, da wani kamfanin zirga-zirgar motoci a China da niyyar shigo da motocin Bus Rapid Transit, BRT a jihar.

Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu ta ce a matakin farko, za a shigo da motoci 100 zuwa jihar don fara zirga-zirgar.

A cewar sanarwar, Gwamnatin Jihar Kano ce ta sa hannu a MoU ɗin da Kano Metropolitan Transport Company, Zhengzhou Yutong Bus Company, China da Zhengzhou Public Bus Communication Co. Ltd., China.

Sanarwar ta jiyo Gwamna Ganduje yana cewa manufar shirin ita ce a kawo juyin juya hali a ɓangaren sufuri a jihar, da kuma sauƙaƙa hanyar yin kasuwanci a birnin dake gaba a kasuwanci a Najeriya.

“A halin yanzu, Kano ita ce jiha mafi yawan al’umma a ƙasar nan. Tana da al’umma da ta wuce miliyan 16. Manya-manyan ababen sufuri su ne ƙananan bas-bas da babura masu ƙafa uku waɗanda ba sa tallafawa ci gaban babban birni.

“Saboda haka, dole a kafa tsayayyen tsarin sufuri na al’umma. Wannan zai nuna matsayin Kano a matsayin babban birni”, a cewar Gwamna Ganduje, wanda Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Aminu Wudil ya wakilta.

A cewar Gwamna Ganduje, Gwamnatin Jihar Kano ta yanke shawarar haɗa kai da Zhengzhou Yutong ne saboda shi ne kamfanin dake samar da motoci mafi girma a duniya, kuma yana da gogewa a harkar sufuri.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnatin Jihar za ta zuba abinda bai gaza kaso 25 cikin ɗari ba a aikin, yayinda Kano Metropolitan Transport Company zai kasance babban mai ruwa da tsaki, Kamfanin Sufurin na China kuma zai kasance mai bada taimakon ma’aikata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan