Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Agajin Kasar Rasha Don Yakar Boko Haram

167


Gwamnatin Tarayya ta nemi had8n kan Kasar Rasha domin kawo karshen yan Tawayen Boko Haram a kasarnan da sauran kasashen da ke gabar tafkin chadi.

Ministan Tsaron kasa Mansur Dan Ali ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a lokacin da ya ke hallartar taron tsaro karo na takwas a birnin Mascow.

Ministan ya kara neman taimakon kasar ta rasha wajen bada gudunmuwar kariya ga yankunan teku na kasarnan da ke gabar tsuburin kasar Guinea.

Minista Dan Ali ya ce ya mika kokon baran ne bayan lura daa ya yi bisa kwarewan kasar Rasha wajen guduanar da harkoki na yakar ta’addanci cikin inganci.

Mansur Dan Ali ya nemi kasar ta kawo mana dauki don kawo karshen aikin ta’addancin Boko Haram da ya ye annobar ta baki daya ta hanyar koyar da dabarun yaki da kuma bunkasa makamai zuwa na zamani da sojoji zasu yi amfani da su.

Ya kara da cewa, akwai damuwa dangane da yadda ta’addanci ke cigaba da karuwa a nahiyar Afirka kamar yadda kungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram ke damun kasar nan da kasashen da ke iyaka da tafkin Chadi, da Kungiyar Al-Shabab a kasashen Somaliya, da Kenya, da Kungiyar ISIS da ke Kasar Mali.

A karshe ministan ya yabawa gwamnatin Kasar Rasha bisa Kokarin ta musamman ta bangaren tallafi da daukar nauyu karatun Yan Najeriya a bangarorin dabam-dabam kamar su Kimiyya, da Fasaha da Likitanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan